Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankin Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji

Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankin Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji

  • Hukumar tattara haraji a jihar Kaduna ta garkame wasu bankuna hudu bisa kin biyan haraji na tsawon shekaru
  • Bankunan an ce sun ki biyan haraji a tsakanin shekarun 2011 da 2020, lamarin da ya fusata gwamnati
  • Gwamnatin jihar ta ce garkame bankunan zai sa wadanda basa biya su sani cewa basu fi karfin doka ba

Hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS), a ranar Alhamis ta garkame rassa hudu na Bankin Fidelity saboda kin biyan sama da Naira miliyan 43.3 na haraji, Daily Nigerian ta ruwaito.

Rassan da aka garkame sun hada da na titin Ali Akilu, Ahmadu Bello Way, hanyar Polytechnic kan mahadar Maimuna Gwarzo, da kuma hanyar Kachia, duk a cikin garin Kaduna.

Ms Aisha Mohammed, mai ba da shawara kan harkokin shari'a kuma sakatariyar hukumar KADIRS, ta shaida wa manema labarai bayan garkamewar a Kaduna, cewa an garkame rassan ne saboda zargin kin biyan kudaden haraji na Naira miliyan 43.3 daga shekarar 2011 zuwa 2020.

KARANTA WANNAN: NDLEA Ta Cafke Dillalan Kwayoyi 89 da Tan 2,800 Na Haramtattun Magunguna a Kebbi

Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankun Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji
Bankin Fidelity | Hoto: banktrack.org
Asali: UGC

Ta bayyana cewa an baiwa bankin sanarwar ta biya harajin har sau biyar, amma ana zargin ya yi watsi da sanarwar.

A cewarta:

“Saboda haka, don neman biyan harajin da ya wajaba zuwa ga jihar, sai muka garzaya kotu muka samo umarnin kotu na garkame rassan.
“Wannan na cikin Sashe na 104 (3) da (4) na Dokar Haraji a Kudin Haraji (Da aka yi wa Kwaskwarima) 2011 da kuma Sashe na 37 (3) da (4) na Dokar Tattara Haraji da Inganta Haraji, 2020 kamar yadda aka gyara."

Manufar garkame ofisoshin kasuwancin da ba sa biyan haraji

Shugaban Hukumar, Dakta Zaid Abubakar ya fada wa manema labarai cewa garkame ofisoshin kasuwanci da ba sa biyan haraji zai tabbatar da bin ka’idojin da suka dace na dokokin haraji a jihar.

A cewarsa, matakin wani bangare ne na kokarin karfafa duk wani biyan haraji cikin dadin rai daga masu biyan haraji, in ji News Diary.

Ya yi kashedin cewa:

“Wannan cikin sauki yana gaya wa duk masu biyan haraji da suka ki biya cewa babu wanda ya fi karfin doka. Ko dai su biya harajinsu, ko kuma doka ba za ta yafe masu ba."

KARANTA WANNAN: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’ai 2 Na Hukumar Shige da Fice Ta ’Immigration’ a Jihar Katsina

Donald Trump ya maka kamfanin Facebook da Twitter a kotu, ya bayyana dalili

A wani labarin, Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a ranar Laraba cewa yana shigar da kara a gaban kotu a kan Facebook, Twitter da Google, yana kara fadada ikrarinsa na 'yancin fadin albarkacin baki da manyan kamfanonin fasahar suka dakile.

An dakatar da Trump daga shafin Twitter da Facebook bayan da wasu gungun magoya bayansa suka mamaye Capitol a wani mummunan hari a ranar 6 ga watan Janairu, inda kamfanonin suka nuna damuwar cewa zai karfafa tashin hankali a kasar, CBSNEWS ta ruwaito.

Trump ya bayyana cewa:

"Muna neman a kawo karshen hana ruwa gudu, a dakatar da garkame bakinmu da kuma dakatar da bakanta sunayenmu, dakatarwa da sokewa da kuka sani sarai.
"Ina da kwarin gwiwa cewa za mu cimma nasarar tarihi ga 'yancin Amurkawa kuma a lokaci guda 'yancin fadin albarkacin baki."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.