Cikakken Bayani: Bayan Sace Sarkin Kajuru, An Sako Ma'aikatan Lafiya da Aka Sace a Yankin

Cikakken Bayani: Bayan Sace Sarkin Kajuru, An Sako Ma'aikatan Lafiya da Aka Sace a Yankin

  • Wasu ma'aikatan kiwon lafiya a jihar Kaduna sun kubuta daga sharrin 'yan bindiga bayan shafe kwanaki 80 a hannunsu
  • Rahoto ya bayyana cewa, an ba da kudin fansa N10m da wasu kayayyaki kafin a ba da fansan mutanen
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka sace Sarkin yankin Kajuru a jihar ta Kaduna a ranar Lahadi

Ma’aikatan jinya biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna sun samu sun kubuta bayan kwanaki 80 da suka yi a hannun 'yan bindiga, Daily Trust ta ruwaito.

Ma'aikatan jinyar, Afiniki Bako da kuma Grace Nkut, an sace su a watan Afrilu, yayin da suke kan aiki dare a Babban Asibitin Doka a Kajuru, yankin Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da labarin, shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM), reshen Jihar Kaduna, Kwamred Ishaku Yakubu, ya ce an sake su ne a ranar Asabar, 10 ga Yuli da misalin karfe 7:00 na dare.

Kara karanta wannan

Bayan Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru, Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzafan Martani

KARANTA WANNAN: Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankin Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji

Da Dumi-Dumi: Bayan Sace Sarkin Kajuru, 'Yan Bindiga Sun Sako Wasu Ma'aikatan Lafiya
'Yan bindiga dauke da makamai | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce babu wani karin kudin fansa da aka biya ga masu garkuwar baya ga naira miliyan 10 da aka biya su tun farko.

Ya ce an ba ‘yan bindigan babura biyu kafin a saki ma'aikatan.

An tattaro cewa masu garkuwan da farko sun karbi naira miliyan 10, 50,000, katin waya na N50,000 da kuma wayar salula kirar Tecno 4 a matsayin fansa.

Bayan Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru, Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzafan Martani

Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Ibrahim Zailani, ya bayyana sace sarkin Kajuru, Alhaji Adamu Kajuru, da wasu yan bindiga suka yi tare da wasu mutum 10 a matsayin abun almara, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya bayyana haka ne a wani jawabi da mai taimaka masa na musamman ta ɓangaren yaɗa labarai, Ibrahim Dahiru Danfulani, ya baiwa manema labarai a Kaduna.

Kara karanta wannan

Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga

Shugaban majalisar dokokin yace labarin sace sarkin Kajuru tare da wasu mutum 10 daga cikin iyalan gidansa abun mamaki ne kuma gwamnati ba zata zauna hakanan ba, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna

A wani labarin, Wasu 'yan bindiga sun sace mutane shida ciki har da yara a garin Milgoma da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Juma’a yayin da 'yan bindigan suka zo da yawa suka afka wa jama'a.

Wani dan acaba da aka kaiwa harin, yanzu haka yana karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.