Hotunan gwamnan Ogun yana gyara cunkoson titi da dare sun janyo cece-kuce

Hotunan gwamnan Ogun yana gyara cunkoson titi da dare sun janyo cece-kuce

  • Gwamna Dapo Abiodun ya shiga kanun labarai a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli bayan ya shiga cunkoson kan titi yana gyarawa da dare
  • Wannan cigaban ya faru ne yayin da gwamnan yake komawa gida daga aiki bayan kammala na ranar Laraba
  • Martani daban-daban ya dinga bayyana kan hakan inda wasu suka dinga kwarzanta shi yayin da wasu ke fatan sauran gwamnoni suyi koyi da shi

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya nuna kaunarsa ga jama'arsa a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli inda ya nuna irin bautar da yake musu.

Yayin da yake komawa daga aiki a ranar, gwamnan ya tarar da gagarumin cunkoson jama'a a yankin Oke-Mosan na jihar. Kamar yadda yace, cunkoson ya faru ne sakamakon gyaran titin da ake a yankin.

KU KARANTA: 2023: Zulum ya goyi bayan gwamnonin kudu kan mika mulki yankinsu

Hotunan gwamnan Ogun yana gyara cunkoson titi da dare sun janyo cece-kuce
Hotunan gwamnan Ogun yana gyara cunkoson titi da dare sun janyo cece-kuce. Hoto daga Prince Dr Dapo Abiodun
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Kotu ta wanke tsohuwar ministan Buhari kan badakalar kwalin NYSC

Ina son in ga ababen hawa na tafiya babu cunkoso

A maimakon ya dakatar da cunkoson da karfin kujerarsa, sai ya sauka kasa inda ya shiga cikin masu gyaran titi yana gyara cunkoso domin ababen hawa su wuce lafiya kalau.

A yayin wallafa hotunan a shafinsa na Facebook, gwamnan ya wallafa: "Daga nan na sauka kuma na shiga cikin jami'an dake kula da cunkoson domin gyara hanya har ababen hawa su samu su wuce."

Wallafar ta janyo martani daban-daban

A yayin rubuta wannan rahoton, wallafar ta janyo sama da jinjina 2,000 tare da tsokaci kala-kala daga 'yan Najeriya.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da jama'a suka yi.

Adekoya Lanre ya ce: "Za ka iya fiye da hakan gwamna. Ka zo wurin Sango kafin kasan gada ta hanya Oju Ore, ba a iya wucewa ta titin."

Kofoshi Bab's yace: "Hakan yasa aka zabeka kuma hakan ne dalilin da yasa kake gwamnan Ogun, Haka kake ci da sha daga kudin harajinsu. Don haka ba sai ka kwarzanta kanka ba gwamna domin aikinka kayi."

A wani labari na daban, shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Farouk Yahaya a ranar Laraba ya ce dakarunsa sun aike da 'yan bindiga masu yawa lahira inda zasu amsawa Ubangiji laifukan da za a tuhumesu dasu.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, babban kalubalen dake addabar kasar nan a halin yanzu shine ayyukan miyagun 'yan bindiga.

A yayin jawabi ga manema labari na gidan gwamnati bayan kara masa girma zuwa mukamin Laftanal Janar, Yahaya ya ce sojoji suna matukar azabtar da 'yan bindiga yanzu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel