Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira

Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira

  • Hukumar kula da lamurran 'yan sanda ta yi watsi da kudirin karin girma ga Ibrahim Magu
  • Hukumar ta sanar da cewa tana jiran umarni daga ministan shari'a da sifeta janar na 'yan sanda
  • Ana zargin Ibrahim Magu da waddaka da wasu kudade tare da kariya ga masu laifi a EFCC

Hukumar kula da lamurran 'yan sanda (PSC), a ranar Alhamis ta yi watsi da kudirin karin girma ga tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu.

Hukumar ta ce tana jiran umarni daga ofishin antoni janar na tarayya da ministan shari'a tare da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: 2023: Zulum ya goyi bayan gwamnonin kudu kan mika mulki yankinsu

Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira
Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira
Asali: Original

Wannan sanarwan na kunshe a wata takarda da aka baiwa manema labarai ta hannun kakakin hukumar, Ikechuckwu Ani.

Daily Trust ta ruwaito cewa akwai rade-radin da ake yi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin karawa Magu girma.

Karin bayani na nan tafe...

KU KARANTA: Da duminsa: Kotu ta wanke tsohuwar ministan Buhari kan badakalar kwalin NYSC

A wani labari na daban, shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Farouk Yahaya a ranar Laraba ya ce dakarunsa sun aike da 'yan bindiga masu yawa lahira inda zasu amsawa Ubangiji laifukan da za a tuhumesu dasu.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, babban kalubalen dake addabar kasar nan a halin yanzu shine ayyukan miyagun 'yan bindiga.

A yayin jawabi ga manema labari na gidan gwamnati bayan kara masa girma zuwa mukamin Laftanal Janar, Yahaya ya ce sojoji suna matukar azabtar da 'yan bindiga yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel