Ta fasu: Magu ya hana bincikar Fintiri da wasu tsoffin gwamnoni 3, Kwamitin Salami

Ta fasu: Magu ya hana bincikar Fintiri da wasu tsoffin gwamnoni 3, Kwamitin Salami

  • Kwamitin bincike ya bankado yadda Magu yake kange binciken wasu tsoffin gwamnoni hudu na rashawa
  • Kamar yadda aka gano, Ibrahim Magu ya hana bincikar Kwankwaso, Donald Duke, Ibikunle Amosun da Fintiri
  • Ibrahim Magu kamar yadda kwamitin Salami yace, ya umarci jami'ai da kada su kuskura su binciko mutum hudun

Ibrahim Magu

Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, an zargesa da kange wasu bincike na zargin rashawa da ake wa wani gwamna mai ci yanzu da wasu tsoffin gwamnoni uku.

Kwamitin Jastis Ayo Salami ya ce yayin da Magu ke shugabantar EFCC, Magu "ya umarci jami'ai da kada su bincike" kan zargiin rashawa kan wasu mutum hudu, TheCable ta ruwaito.

Tsoffin gwamnonin an gano sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano, Donald Duke na jihar Cross River da Ibikunle Amosun na jihar Ogun wanda yanzu haka sanata ne.

KU KARANTA: Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Dilip Kumar ya riga mu gidan gaskiya

Ta fasu: Magu ya hana bincikar Kwanwaso da wasu gwamnoni hudu, Kwamitin Salami
Ta fasu: Magu ya hana bincikar Kwanwaso da wasu gwamnoni hudu, Kwamitin Salami. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Hotunan Buhari yana kawata sabon COAS, yana jagorantar FEC a Aso Villa

Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, wanda a halin yanzu yake jagorantar jihar yana daga cikin fitattun 'yan siyasa wadanda Magu ke kangewa daga bincike.

An umarci Malami da ya binciki Magu tare da gurfanarwa

Abubakar Malami, antoni janar na tarayya wanda tun farko ya bada shawarar tsige Magu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, an bukaci ya cigaba da bincike tare da gurfanar da tsohon shugaban EFCC kan laifukan da kwamitin suka binciko nashi.

Bayan korafin da Malami ya mika ga Buhari, kwamitin binciken ya binciki Magu inda aka maye gurbinsa da sabon shugaba a hukumar bayan an gano yana amfani da kujerarsa ba yadda ya dace ba.

Tsohon shugaban EFCC ya musanta duk wasu zarginsa da ake yi koda ya bayyana a gaban kwamitin bincike, TheCable ta ruwaito.

A wani rahoto da aka mika a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, an zargi tsohon shugaban hukumar da batar da shaidu, tsaida bincike da hana wasu binciken rashawa tare da batar da duk wata shaida da za ta sa a kama wanda ake zargi.

A wani labari na daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sake yin kira da a mika mulki yankin kudancin kasar nan inda ya goyi bayan zauren gwamnonin kudanci a matsayarsu ta zaben yankin da zai yi shugabancin kasa a 2023.

A wani taro da gwamnonin kudancin suka yi a Legas a ranar Litinin, sun aminta da cewa yankinsa ne ya dace ya fitar da shugaban kasa na gaba idan za a duba adalci da daidaito, lamarin da Zulum ya bada goyon baya.

"Na fadi ba sau daya ba ko biyu, Ni Farfesa Babagana Zulum, na tsaya a matsayar cewa a mika shugabancin kasa zuwa yankin kudu a 2023 saboda hadin kan kasar nan yana da amfani," gwamnan ya sanar a wata tattaunawa da aka yi da shi a Channels TV a shirin gari ya waye na ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng