Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo

Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo

  • Mallam Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo ya yi martani a kan mukabalar da ya gudana tsakaninsu da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
  • A cewar malamin, duk wani masoyin Annabi da sahabbansa zai yi kwanan farin ciki a yau saboda cewa Allah Ya kunyata shi tun a duniya
  • Mallam Rabi'u ya ce a cikin dukka tambayoyin da suka yi masa, babu ko guda da ya iya amsa

A yau Asabar, 10 ga watan Yuli ne aka yi zaman mukabala tsakanin fitaccen malamin nan na Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da malaman jihar wanda gwamnati ta shirya.

An shafe kimannin awanni biyar ana fafatawa tsakanin malaman da Abduljabbar kafin aka kawo karshen zaman.

KU KARANTA KUMA: Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi

Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Asali: Facebook

Sai dai an tattaro cewa a duk tambayoyin da aka yiwa Shehin Malamin babu ko guda da ya amsa kamar yadda Mallam Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan masu ruwa da tsaki na APC sun marawa Sanata Musa baya domin ya zama Shugabansu na kasa

A wata hira kai tsaye da Mallam Muhammad ya watsa a shafin nasa an jiyo yana cewa:

“Mun gode wa Allah Madaukakin sarki da ya raya mu zuwa wannan rana mai albarka, ranar da aka zauna da Abduljabbar kan irin maganganun da yake yi yana danganawa Sahabban Annabi SAW da malaman Musulunci da nuna cewa sune suke irin wadannan maganganu.
“Alhamdulillah kamar yadda ya nema da kansa cewa ayi zama da shi, hukuma ta amsa kuma dama muma wannan shine abun da muke so. Alhamdulillah an yi zama lafiya an kuma tashi lafiya.
“A yau dukkan wani masoyin Annabi sahabbansa zai kwana cikin farin ciki da jin dadi ta yadda tun a nan duniya Allah ya Madaukakin sarki ya kunyata wanda yake nasabta munanan kalmomi ga fiyayyen halitta, ko ya nasabta munanan kalmomi ga fiyayyen halitta sai yace sahabban Annabi ne suka fada. Ko ya ce Imamul-Buhari ne ya kawo ko ya ce Imamul-Musulim ne ya kawo.

Kara karanta wannan

Jerin tambayoyin da aka jefawa Sheikh Abduljabbar Kabara da martanonin da ya bada

“Alhamdulillah mun bijiran masa da mas’aloli guda shida a karkashin kowaccce akwai tambaya bazata gaza guda hudu ba. Ba ko daya wanda ya amsa a ciki, ba guda daya da ya iya amsawa.
“Wani abun mamaki ta inda za a gane wannan mutumi karya yake yiwa malamai, karya yake yiwa sahabbai,ka ce a cikin littafi ta kaza a lambar hadisi ta kaza Anas dan Maliki Allah ya kara yarda a gareshi ya ce Annabi SAW yayi fyade ga daya daga cikin matansa Nana Safiyya Allah ya kara mata yarda (wa’iyyazubillah) ka fadi lamba amma an ce ka budo an fada maka lambar an nanata, ance budo ka karanta amma abu ya gagara, wannan yana nuna cewa dama abun da kake fada karya ne.”

Martanin jama'a kan sharhin:

Zainab Adamu ta ce:

"Allah ya saka muku da alkhairi malaman ahlil sunnah na kano. Abdul jabbar Allah ya shiryeka idan na shiryiwa ne. Malaman kano Allah ya biya ku da gidan Aljannatul firdaus. Aameen da addu'a malam."

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Tambuwal ya lallashi matasa a jihar Sakkwato, ya ce ana bincike kan mai laifin

Shehu Sidi ya ce:

"TSmmmmm.Babu gaskiya ga wannan batun naka.Film ne kawai gwamnati ta tsara,domin ta halastarma kanta cigaba da zalumtar sheikh Abduljabbaar."

Abdulwahab Abdulrazaq ya yi martani:

"Karyar banza kawai gamasu zagin annabi afili amatsa yinku na malamai bakudau matakiba sai akan mutum daya dayake sangera kuketa hayaniya wlh kuji tsoron Allah."

Ibrahim S Dankaka Gabari ya ce:

"Masha Allah, tundaga nan duniya ya fara ganin abinda ya girba wannan masu tambayar duniya kinan inaga anje kiyama. Allah ka tsare mana imanin mu."

AbdulJabbar da Malaman Kano: Bayan kimanin awanni 5, an kammala mukabalar

A baya Legit.ng ta kawo cewa bayan kimanin awanni biyar ana tattaunawa kan maganganun da ake zargin Malam AbdulJabbar Kabara da yi, na kawo karshen zaman.

KU KARANTA KUMA: Batanci ga Annabi: Tambuwal ya lallashi matasa a jihar Sakkwato, ya ce ana bincike kan mai laifin

Bayan sauraron duka bangarorin biyu, Alkalin mukabalar, shugaban jami'ar Al-Istiqamah Farfesa Salisu Shehu ya ce babu tambayar da Abdul Jabbar ya amsa cikin tambayoyin da akayi masa.

Kara karanta wannan

AbdulJabbar da Malaman Kano: Bayan kimanin awanni 5, an kammala mukabalar

Ya mika lamarin yanzu ga gwamnatin jihar Kano domin ta yanke shawararta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel