‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’ai 2 Na Hukumar Shige da Fice Ta ’Immigration’ a Jihar Katsina

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’ai 2 Na Hukumar Shige da Fice Ta ’Immigration’ a Jihar Katsina

  • Wasu 'yan bindiga sun yi bata kashi da jami'an tsaro sun hallaka wasu jami'an hukumar shige da fice mutum biyu
  • An ruwaito cewa, wani soja da ya kawo dauki shi ma an harbe shi a cinya, yana karbar kulawar asibiti
  • Hukumar ta shiga da fice reshen jihar bata bayyana komai akan lamarin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun harbe wasu jami’an hukumar shige da fice ta kasa (NIS) har mutum biyu a cikin jihar Katsina.

An bayyana sunayen jami’an da Umar Bagadaza Kankara da Lauwali Dutse.

Lamarin wanda ya faru da sanyin safiyar ranar Alhamis da misalin karfe 12:05 na safe, ya faru ne a kauyen Kadobe, dake karamar hukumar Jibia.

KARANTA WANNAN: Ministan Tsaro Ya Yi Sharhin Kalaman Buhari Na ‘Yaren da Suka Fi Fahimta’

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’ai 2 Na Hukumar Shige da Fice Ta ’Immigration’ a Jihar Katsina
Jami'an hukumar NIS | Hoto: nigerianguide.com.ng
Asali: UGC

An tattaro cewa musayar wutar da ta biyo bayan lamarin ya jawo mutuwar ‘yan bindigar da dama, kuma da yawa daga cikinsu sun samu raunuka daga harbin bindiga.

Wani soja, wanda yana daga cikin wadanda suke aikin karfafa doka a yankin, ya samu harbin bindiga a cinyarsa, yanzu haka yana karbar magani a asibitin tarayya dake Katsina.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa The Guardian cewa NIS tana da tushe a kauyen da abun ya faru, tare da bayyana yankin a matsayin mafakar makiyaya da dabbobinsu da yawa.

Lokacin da aka tuntube shi, mai magana da yawun hukumar ta NIS a jihar, Illyasu Kasimu, ya ce ba a bashi izinin yin magana a kan lamarin ba.

Matasan Katsina sun shirya horar da yadda za a fatattaki 'yan bindiga

Matasa a jihar Katsina sun shirya wani horo kan yadda ake amfani da bakan danko don yakar hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a jihar, The Cable ta ruwaito.

An sha samun hare-hare da dama daga ’yan bindiga a kan al’umomin da ke jihohin arewa, wanda ke haifar da sace-sacen mutane da kashe-kashe da dama.

Matasan, wadanda suka bayyana kansu a matsayin mambobin kungiyar sada zumunta ta jam'iyyar PDP a jihar Katsina, sun ce an shirya horon ne domin kare mazauna yankin daga barnar ‘yan bindiga.

KARANTA WANNAN: Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Wani Babba a Jami'iyyar APC

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kai hari a wani wurin fasa duwatsu a kauyen Ugya da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa, inda suka kashe wani ma’aikaci a wurin, Ibrahim Aliyu, tare da yin awon gaba da wani, Abdul Umar Ekuji.

Wani mazaunin yankin, mai suna Salihu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:43 na yamma a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogin AK47 sun mamaye wurin da ake fasa duwatsun, wanda ya ce yana da nisan kilomita biyu da bainar jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel