Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido
- Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa ya ce babu yadda za a yi mutanen da ke karkashin Buhari su yarda Tinubu ya zama Shugaban Kasa
- A cewarsa saboda kwarewar shugabancin Tinubu idan suka bari ya zama Shugaban Kasa zai shafe nasarorin gwamnatin Buhari
- Sannan ya ce gwamnatin Buhari ta gaza ta kowace fuska
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya yi ikirarin cewa magoya bayan Shugaba Muhammad Buhari na adawa da yiwuwar tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa Bola Tinubu ya zama Shugaban Kasa a 2023.
Da yake magana a Kano yayin zantawa da wadansu zababbun manema labarai, jigo a Jam’iyyar PDPn ya ce wadanda suka tallata Shugabancin Buhari tabbas za su yi watsi da takarar Tinubu a 2023, suna tsoron kada fitowar sa ta dusashe aikinsu na shekara 8 sannan kuma ya goge ayyukan da suka yi a tarihi.
A cewar Lamido:
“A 2023, yanayin siyasar da ke kunno kai shi ne duk wani mai nagarta, ba za su sanya shi a takarar ba. Idan ka sa Tinubu a wajen, to zai dusashe nasarorin Buhari.
‘‘Ina fadar hakan saboda Tinubu yana sane da abin da yake yi, ya san abin da yake yi a matsayinsa na shugaba. Yana gina mutane, ya gina tattalin arziki. Yana da abubuwa da yawa a gare shi, kawai dai suna masa hassada.
“Don haka, ba za su taba ba shi damar kai wa Fadar Shugaban Kasa ba saboda idan ya kai mukamin, nasarorin nasa za su binne na Buhari ne kawai kuma su kara fito da batun Shugabancinsa maras ma'ana. Ba za su ba shi damar ba,”
DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos
KU DUBA: A tarihin Najeriya, babu gwamnatin ta taba jin kan talakawa irin ta Buhari, Gwamna Masari
Lamido, wanda ya ce gwamnatin Buhari ta gaza matuka ta fuskoki daban-daban daga kan batun tsaro zuwa tattalin arziki, gami da yadda take tunkarar rikice-rikicen da ke faruwa a kasar nan a halin yanzu, ya yi nadamar cewa duk wadannan matsalolin sun samo asali ne daga mummunan shugabanci.
Lamido ya ce ya kamata shugaban Najeriya ya iya amfani da matakan jagoranci na gari kamar yadda aka fayyace a cikin dukkanin littatafan addini, yana mai cewa da zarar an yi hakan, abubuwa za su gyaru kuma Najeriya za ta dawo kan turba.
Kungiyoyin Arewa sun gindaya wa kudu sharadin samun shugabancin kasa a 2023
Shawarar da gwamnonin kudu suka yanke na hana kiwo a fili a yankin bai samu karbuwa ba sosai daga wasu kungiyoyin arewa.
Harma, kungiyar cigaban Fulani ta Gan Allah (GAFDAN) ta ce matsayin gwamnonin zai zo da wasu munanan kalubale da zasu haifar a kasar.
Alhaji Ibrahim Abdullahi, sakataren kungiyar GAFDAN na kasa, ya fadawa jaridar Nigerian Tribune cewa haramcin zai kawo cikas ga yankin musamman a zaben shugaban kasa na 2023.
Asali: Legit.ng