Babu Wasu Yan Ta'adda da Zamu Kyale Ba Tare da Mun Hukunta Su Ba, Buhari

Babu Wasu Yan Ta'adda da Zamu Kyale Ba Tare da Mun Hukunta Su Ba, Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sha alwashin hukunta duk wani ɗan ta'adda
  • Buhari ya nuna alhininsa bisa mummunan harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai jihar Adamawa
  • Shugaban ya jajantawa iyalan waɗanda abun ya shafa, tare da alƙawarin taimaka musu

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna rashin jin daɗinsa bisa kisan gilla da aka yi wa wasu yan Najeriya da suka haɗa wani shugaban yan tawagar bijilanti da dagacin ƙauyen Dabna, ƙaramar hukumar Hong, jihar Adamawa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu

Da yake martani kan lamarin, shugaba Buhari yace "Wannan ta'asar, rashin imani, da rashin mutunci dake ɗaukar rayuwar mutane ba zai tafi hakanan ba."

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Babu Wasu Yan Ta'adda da Zamu Kyale Ba Tare da Mun Hukunta Su Ba, Buhari Hoto: @MuhammaduBuhari
Asali: Instagram

A wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis, Buhari ya umarci jami'an tsaro cewa "ku ninka ƙoƙarin da kukeyi wajen ɗaukar mataki a kan wannan barazanar tsaron cikin gaggawa."

"Ba zamu amince mu baiwa yan Najeriya kunya ba dangane da amanar da suka danƙa a hannun mu na tsare rayuwarsu." inji shi.

Gwamnati zata tallafawa iyalan waɗanda abun ya shafa

Vanguard ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya umarci hukumomin da abun ya shafa ƙarƙashin jagorancin ma'aikatar jin ƙai da walwala da su gaggauta gano abubuwan da aka rasa a waɗannan yankuna kuma su tura da tallafin gwamnati.

KARANTA ANAN: Karin Bayani: Jerin Sunayen Sabbin Shugabannin Jami'o'in FG da Shugaba Buhari Ya Naɗa

A halin yanzun, shugaba Buhari ya kafa tawagar wakilai da zasu ziyarci yankin da harin ya shafa tare da ta'aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe da kuma gwamnatin Adamawa.

A wani labarin kuma Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata shirya wa ma'aikatan SPW horo na musamman a kan ƙananan sana'o'i.

Gwamnatin tace zata shirya wannan bayad da horon ne a kowace mazaɓar sanata dake faɗin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel