Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu

Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu

  • Hukumar makarantar Bethel Baptist ta ce ta kaiwa yan bindiga buhun shinkafa 9 amma sun ƙi amsa
  • Yan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar a Kaduna sun nemi iyaye da hukumar makarantar su bada abinci
  • Sun bayyana cewa hukumomin tsaro sun toshe musu duk wata hanya da suke samun abinci

Yan bindigan da suka sace ɗalibai a makarantar sakandire ta Bethel Baptist, sun yi watsi da buhunan shinkafa 9 da sauran kayan abinci da hukumar makarantar ta kai musu, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega, a Sabon Muƙami

Mataimakin shugaban makarantar, Wakili Madugu, shine ya bayyana haka a wata fira da yayi da gidan radiyon 'Nigerian Info Abuja' ranar Alhamis.

Madugu, yace maharan sun kira shi a waya da misalin ƙarfe 7:30 na safe ranar Talata, sun tabbatar da cewa yaran suna cikin ƙoshin Lafiya.

Yan bindiga sun ƙi amsar buhun shinkafa 9
Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Yi Watsi da Buhun Shinkafa 9 da Aka Kai Musu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yan bindigan sun nemi makaranta ta basu abinci

Hukumar makarantar ta bayyana cewa ɓarayin sun buƙaci a basu kayan abinci da zasu ciyar da ɗaliban dake hannunsu.

Mr. Madugu ya ƙara da cewa ɓarayin sun ce hukumomin tsaro sun hana su hanyoyin samun abinci, sabida haka suka nemi makaranta da iyayen yaran su samar da abinci.

Yace: "Sun buƙaci mu basu buhunan shinkafa yar ƙasar waje guda 10 da buhu 20 na yar gida, Buhu 20 na wake, katan 10 na maggi, Jarka 10 na mai da kuma jaka 2 na gishiri, wannan sune abinda suka buƙaci mu basu."

KARANTA ANAN: Rikicin Siyasa: Jam'iyyar APC Ta Gayyaci Ministan Buhari Kan Wani Zargi

Madugu ya bayyana cewa makarantar ba ta da wannan kayan abincin da suka nema saboda ana shirin tafiya hutu a mako mai zuwa ne lamarin ya faru.

Ya bayyana cewa hukumar makarantar ta yi ƙoƙarin bada abunda take da shi a hannu, amma yan bindigan suka ƙi amsa.

A wani labarin kuma Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Gwamna Zulum na jihar Borno , yace dokar hana fulani makiyaya kiwo a fili ba za ta yi aiki ba.

Gwamnan yace abinda ya kamata a maida hankali akai shine lalubo hanyar magance matsalar tsaro da ta abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel