Jagoran APC a Zamfara: Yari da Marafa basu yarda da jagorancin Matawalle ba

Jagoran APC a Zamfara: Yari da Marafa basu yarda da jagorancin Matawalle ba

  • Jiga-jigan APC a jihar Zamfara, Abdulaziz Yari da Kabiru Marafa sun nuna adawa da jagorancin jam'iyyar na jihar da aka damka wa Matawalle
  • Sun bayyana cewa ba zai yiwu wani daga Abuja ya bayar da umurnin rusa jam'iyyar tare da nada sabon shugaba ba
  • Gwamna Mai Mala Buni dai ya ayyana Gwamna Bello Matawalle a matsayin shugaban APC a Zamfara bayan ya sauka sheka daga PDP

Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, da Sanata Kabiru Marafa, sun yi tur da batun cewa Gwamna Bello Matawalle ne shugaban APC a jihar.

Jiga-jigan na Jam’iyya mai mulki sun bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

Jagoran APC a Zamfara: Yari da Marafa basu yarda da jagorancin Matawalle ba
Yari da Marafa basu yarda da jagorancin Matawalle a Zamfara ba Hoto: Governor Bello Matawalle
Asali: Facebook

Idan za ku tuna, Shugaban riko na APC, Mai Mala Buni ya ayyana Gwamna Matawalle a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar Zamfara bayan ya sauya sheka daga PDP.

Ba zai yiwu ace an rusa shugabancin jam'iyya ba

Sai dai kuma Yari da Marafa sun nuna adawa da jagorancin jam’iyyar da aka damka wa Matawalle, inda suka ce hakan ba mai yiwuwa bane.

“Abu guda ne ba mu lamunta da shi ba, inda Buni ya ce Matawalle ne shugaban APC saboda a lokacin da muka tattauna da gwamnoni guda shida babu shi a ciki.
"Abunda muka aminta da shi shine a je a kaddamar da Bello a dawo. Amma da muka je an yi takkadama mun tarar da an yi tsari in ji wasu cewa idan an je a ruguza jam’iyya. Ba a rushe jam’iyya ba domin babu wanda ke da ikon ruguza ta,” in ji Yari.

KU KARANTA KUMA: Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martani

A bangaren Marafa ya ce daura Gwamna Matawalle a matsayin shugaban APC a Zamfara wata yaudara ce da ba su yarda da ita ba.

Ya jadadda cewa zancen banza da wofi ne wani ya zauna a Abuja ya ce ya ruguza jam’iyya tare da nada wani shugaba.

A karshe Tinubu ya karya shirunsa, ya yi martani kan sauya shekar Matawalle zuwa APC

A gefe guda, Asiwaju Bola Tinubu, babban jigon APC na kasa, ya yi wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, maraba da zuwa jam'iyyar mai mulki.

Tsohon gwamnan na Legas ya yaba wa Matawalle kan yadda bai mika wuya ga tursasawa da matsin lamba da jam'iyyar PDP ta yi masa don hana shi sauya shekar ba, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu a cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Tunde Rahman, ya ce aikin Gwamna Matawalle ya nuna cewa ya dukufa wajen kawo kyakkyawan shugabanci a jiharsa.

A wani labari na daban, mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya soki tsofaffin abokan aikinsa a jam’iyyar PDP, da su ka sauya-sheka, su ka bi tafiyar APC mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Gwamna Nyesom Wike ya na cewa gwamnonin da su ke barin PDP, su na shiga jirgin APC, ba su san abin da ya kamata ba.

Nyesom Wike ya yi wannan magana ne bayan ya fara jin rahoton cewa mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle zai fice daga jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel