APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

  • Jam'iyyar APC ta yi watsi da zargin cewa tana shirya maguɗin zaɓe a babban zaɓen 2023 dake tafe
  • Shugaban PDP, Uce Secondus, shine ya zargi jam'iyya mai mulki da ƙoƙarin komawa kan mulki ko ta halin yaya
  • APC tace gwamnatin shugaba Buhari ta samar da kayayyakin zaɓe na zamani da zasu hana duk wani shiri na canza sakamakon zaɓe

Jam'iyya mai mulki APC ta yi watsi da zargin jam'iyyar adawa PDP ta mata cewa tana shirin yin maguɗi a babban zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Taya Matawalle Murna, Ya Faɗi Dalilin Gwamnan Na Sauya Sheƙa Zuwa APC

APC tace idan aka duba tarihin ta da na abokiyar hamayyar ta za'a gano ainihin waye ya saba yin maguɗin zaɓe.

Jam'iyyar ta kara da cewa ita da take da mambobi waɗanda suka yi rijista da ita kimanin mutum miliyan 40m, maguɗin zaɓe ba nata bane.

APC Ta Yi Zazzafan Martani
APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da sakataren kwamitin riƙo na jam'iyyar APC, Sen. John James Akpanudoedehe, ya fitar ɗauke da sanya hannunsa.

Yace: "Ba gaskiya bane zargin da shugaban PDP, Uche Secondus, yayi wa jam'iyyar mu ta APC cewa muna shirin yin maguɗi a zaɓen 2023 dake tafe."

"Muna son yan Najeriya su tuna cewa kusan dukkan mambobin APC an taɓa murɗe musu zaɓe a lokacin da PDP ke kan madafun iko."

"Amma gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta samar da kayayyakin zabe na zamani waɗanda zasu taimaka wajen magance haka nan gaba."

KARANTA ANAN: Labari Cikin Hotuna: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru

PDP na jin tsoron zata sha kaye ne a zaɓen 2023

Sakataren APC ya ƙara da cewa jam'iyyar dake da mambobi kimanin 40 miliyan me zai sa tayi tunan maguɗin zaɓe.

Yace: "APC tana aiwatar da ayyuka da shirye-shirye masu kyau kuma dai-dai da buƙatun yan Najeriya, wanda hakan ke jawo hankalin mutane da dama su shigo jam'iyyar a dama da su."

"Kawai dai PDP na jin tsoron zata sha kaye ne a duk wani zaɓe dake tafe saboda rashin iya shugabancin ta."

A wani labarin kuma NANS Ta Gana da Sheikh Gumi, Ta Buƙaci a Saƙo Ɗaliban da Aka Sace

Ƙungiyar NANS ta ƙasa ta gana da shahararren malamin nan dake Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Gumi, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Shugaban ƙungiyar, Sunday Asefon, yace sun tattauna da malamin ne domin ganin an kuɓutar da dalibai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel