A karshe Tinubu ya karya shirunsa, ya yi martani kan sauya shekar Matawalle zuwa APC

A karshe Tinubu ya karya shirunsa, ya yi martani kan sauya shekar Matawalle zuwa APC

  • Jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, ya yaba wa Gwamna Matawalle na Zamfara kan dawowa jam’iyya mai mulki
  • Tinubu ya shawarci gwamnan na jihar Zamfara da ya yi aiki tare da gwamnatin Buhari don magance matsalolin kasar
  • Fitaccen jigon na APC ya kuma ce kofofin jam’iyyar a bude suke ga wasu masu sha’awar ci gaban dimokiradiyya a Najeriya

Asiwaju Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya yi wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, maraba da zuwa jam'iyyar mai mulki.

Tsohon gwamnan na Legas ya yaba wa Matawalle kan yadda bai mika wuya ga tursasawa da matsin lamba da jam'iyyar PDP ta yi masa don hana shi sauya shekar ba, jaridar The Guardian ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: APC Ta Yi Zazzafan Martani Kan Shirin Maguɗin Zaɓen 2023, Ta Bankaɗo Wani Sirrin PDP

A karshe Tinubu ya karya shirunsa, ya yi martani kan sauya shekar Matawalle zuwa APC
Jigon APC, Bola Tinubu ya yi wa Matawalle maraba da dawowa jam'iyyar Hoto: Governor Bello Matawalle, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu a cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Tunde Rahman, ya ce aikin Gwamna Matawalle ya nuna cewa ya dukufa wajen kawo kyakkyawan shugabanci a jiharsa.

Sanarwar ta ce:

“Tare da duk sauran yan jam’iyyar APC, ina matukar maraba da gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara zuwa cikin APC. Matakin da Gwamna Matawalle ya dauka ya nuna cewa ya dukufa wajen kawo kyakkyawan shugabanci a jiharsa kuma babbar hanyar yin hakan ita ce kasancewa dan jam'iyyar da aka kafa ta bisa akida ta dimokiradiyya da kuma burin samar da ingantacciyar kasa ga dukkan mutanen Nigeria.
“Wannan jam’iyyar ita ce APC don tana wakiltar mafi inganci na yanzu da kuma na nan gaba.
"Kamar yadda gwamnoni David Umahi na jihar Ebonyi da Ben Ayade na Kuros Riba suka yi kafin shi, Gwamna Matawalle ya bijirewa tursasawa da matsin lambar PDP don ci gaba da kasancewa tare da ita."

KU KARANTA KUMA: Sai wanda bai san ciwon kansa ba zai zauna a jam’iyyar PDP inji Injiniya Buba Galadima

Shugaban na APC ya karfafa wa Gwamna Matawalle gwiwa a yanzu da ya kara yin aiki tare da hada kai da Shugaba Muhammadu Buhari don taimakawa wajen tabbatar da ci gabansa da kuma tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.

A wani abin da ke zama sako ga sauran gwamnonin PDP, Tinubu ya ce kofofin jam’iyya mai mulki a bude suke ga wadanda ke son dimokradiyya ta bunkasa.

Ya ce:

"Shigowar Gwamnoni Matawalle, Umahi da Ayade cikin jam'iyyar ya nuna cewa lallen APC a takaice yake don karbar duk wadanda ke da kyawawan ra'ayoyi da gudummawa ga jam'iyyar da kasarmu."

Sauya Sheka: Rashin damokaradiyyar cikin gida ta sa gwamnoni ke tserewa, APC ga PDP

A gefe guda, a ranar Laraba da ta gabata, jam'iyyar APC tayi martani kan zargin da ake yi na cewa komen da wasu gwamnonin PDP ke yi zuwa APC hanya ce ta buga magudin zabe a 2023.

Premium Times ta ruwaito cewa a wata takarda da APC ta fitar ta hannun sakataren jam'iyyar na kasa, John Akpanudoedehe, ta ce 'yan jam'iyyar PDP na barin jam'iyyar ne tare da komawa APC saboda rashin adalci da suke fuskanta da kuma rashin damokaradiyyar cikin gida.

Wannan martanin ya biyo bayan zargin da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus yayi bayan sauya shekar da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle yayi zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel