Matawalle: Rikakken Gwamnan PDP ya ce ko shi kadai ya rage a Najeriya, ba zai shiga APC ba

Matawalle: Rikakken Gwamnan PDP ya ce ko shi kadai ya rage a Najeriya, ba zai shiga APC ba

  • Gwamnan Ribas ya soki Gwamnan Zamfara saboda ya bar jam’iyyar PDP
  • Nyesom Wike ya yi habaici, ya ce: ‘Mutumin da ya gagara cin zabe a 2019’
  • Bisa dukkan alamu gwamnan ya na Allah-wadai da Gwamnan Zamfara ne

Mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya soki tsofaffin abokan aikinsa a jam’iyyar PDP, da su ka sauya-sheka, su ka bi tafiyar APC mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Gwamna Nyesom Wike ya na cewa gwamnonin da su ke barin PDP, su na shiga jirgin APC, ba su san abin da ya kamata ba.

Nyesom Wike ya yi wannan magana ne bayan ya fara jin rahoton cewa mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle zai fice daga jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Babu abin da APC ta tsinana a mulki sai sace Jihohinmu - PDP

Da yake jawabi wajen kaddamar da aikin titin Woji-Aleto-Alesa da wata gada da za a gina zuwa kamfanin tatar danyen mai, Wike ya tofa albarkacin bakinsa.

Gwamnan na jihar Ribas yake cewa wadanda su ke barin jam’iyyarsu bayan ta yi masu sanadiyyar cin zaben zama gwamnonin jihohi, sun ci amana.

Wike yake cewa akwai munafunci a lamarin jam’iyyar APC mai mulki ta yadda ta ke yin awon-gaba da gwamnonin PDP da ta yi ta caccaka a lokacin baya.

Punch ta rahoto gwamnan ya na habaici a ranar Talata, inda ake tunani da gwamnan Zamfara yake.

Gwamnonin PDP
Matawalle da Nyesom Wike a taron Gwamnonin PDP Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Yari ya yi biyayya ga Jam’iyya bayan an karbe APC a hannunsa

Nyesom Wike ya yi habaici

“Mutanen da zabe kurum wannan sun gagara ci. Jam’iyya ta yi amfani da dabaru, ta je kotu, kuma ta samu nasara. Yanzu za su ce sun bar jam’iyyar.”
“Mutane marasa kunya, wadanda ba su tunanin kai ga ci. Mutanen da ba su san dama da hagunsu ba.”

Shi ma gwamnan ya ce karfa-karfa ake yi wa gwamnonin PDP, su sauya-sheka zuwa APC mai mulki, ya ce amma shi babu abin da zai fitar da shi daga PDP.

“Ku yi duk abin da za ku yi mani, ba zan bi ku ba (zuwa APC). Ribas ba za ta bi ku ba, ko da Ribas ce kadai ta rage a kasar nan, za mu yi zamanmu a PDP.”

A jiyan ne aka ji cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, murnar sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Hakan na zuwa a lokacin da Prince Uche Secondus yake zargin gwamnati da sace Jihohin PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel