Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martani

Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martani

  • Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan maganganun da PDP ke yi na zargin kitsa magudi daga APC
  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa, babu wata manakisa da take kitsawa a zaben 2023 mai zuwa
  • Ta kuma bayyana dalilan da suka sanya PDP ke rashin mambobinta, da kuma rashin tsarinta

Jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da zarge-zargen da ke danganta ficewar wasu gwamnoni daga jam'iyyar PDP da kitsa wani makircin magudi a babban zaben shekarar 2023.

PDP ta sake fuskantar wani mummunan rauni a ranar Talata saboda sauya shekar da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi zuwa APC, Premium Times ta ruwaito.

A martanin da ya mayar, Shugaban PDP na Kasa, Uche Secondus, ya ce ficewar ta gwamna Matawalle ko ta gwamnonin da suka gabata bai dami jam'iyyar ba. Ya zargi jam’iyya mai mulki da jawo gwamnoni don yin magudin zabe.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Hasala, Ta Garzaya Kotu Domin Dakatar da Matawalle Daga Komawa APC

Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar Da Martani
Jam'iyyar PDP da ta APC | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mista Secondus ya yi barazanar bin diddigin duk wata hanyar da doka ta tanada don ganin an karbo hakkin PDP da Kotun Koli ta ba gwamna Matawalle bayan zaben 2019 a Jihar Zamfara.

Amma, APC a cikin wata sanarwa daga Sakataren rikon kwarya na kasa, John Akpanudoedehe, a ranar Laraba, ta yi watsi da zargin da aka yi na kitsa magudi a zaben 2023 da Mista Secondus ya yi.

Ya yi ikirarin cewa mambobin da suka fice daga PDP, ciki har da gwamnoni, suna shiga APC ne saboda "rashin dimokiradiyya da adalci na tantancewa" a jam'iyyar.

“Muna so mu tunatar da 'yan Najeriya cewa yayin da mambobin APC da yawa suka sha wahala a lokacin da PDP ke mulki, APC ba ta da tarihin yin magudin zabe.

Ya kara da cewa:

"Gwamnatin da Muhammadu Buhari ke jagoranta ta gabatar da sauye-sauyen zabe da nufin tabbatar da cewa duk wata baraka da za ta bude a hanyoyin gudanar da zabe don yiwuwar cin zarafi a zabubbukan da ke tafe an rufe su, an kuma kawar da su.”

Mista Akpanudoedehe ya ce babbar jam'iyyar adawar a yanzu:

"Ta kasance za ta gaza saboda hadin kan ta ya samo asali ne daga samun dama a albarkatun kasa."

Yawan ku Ba Zai Hana Mu Karbar Mulki a 2023 Ba, PDP Ta Caccaki Gwamnonin APC

Jam’iyyar PDP ta ce ba ta damu da sauya shekar da gwamnoni a karkashin jam’iyyar suka yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba, tana mai cewa tana da kyakkyawan shiri na karbe kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Gwamna Bello Mattawalle na jihar Zamfara a hukumance ya koma APC daga PDP a ranar Talata, ya zama gwamna na biyu da ya bar babbar jam’iyyar adawar zuwa jam’iyya mai mulki bayan wata daya kacal da takwaransa na jihar Kuros Riba Ben Ayade ya koma APC.

Amma PDP ta nace cewa ficewar ba wani abin damuwa ba ne, tana mai cewa APC ba ta cika alkawuran da ta yi wa ’yan Najeriya ba, Channels Tv ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Ja Kunnen Gwamna Matawalle Kan Komawa APC, Ta Ce Za Ta Kwace Kujerarsa

Yadda PDP Ta Mulki Jihohi 31 Shekaru 14 da Suka Gabata da Yadda APC ta Kwacesu

A wani labarin, A ranar Talata, Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya koma jam'iyyar APC a hukumance. An zabi Matawalle ne a karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Punch ta ruwaito.

Lamarin sauya shekar gwamna Matawalle ya jawo cece-kuce, inda jam'iyyar PDP ta zargi jam'iyyar APC da zawarcin gwamnonin PDP a boye tare da yi tsorata domin shiga jam'iyyar da karfi, jaridar Punch ta tattaro.

Sai dai, jam'iyyar PDP ba karamar jam'iyya bace da bata saba mulki a Najeriya ba, akalla, ta yi mulkin shekaru 16 kafin wata jam'iyya ta karba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel