Tambuwal da Gwamnoni 10 da za su iya jarraba sa’ar hawa kujerar Shugaban kasa a 2023

Tambuwal da Gwamnoni 10 da za su iya jarraba sa’ar hawa kujerar Shugaban kasa a 2023

Yayin da ake dumfarar 2023, wasu ‘yan siyasa sun fara kulle-kullen yadda za ta kaya. Akwai wasu gwamnoni da ake tunani suna kwadayin kujerar shugaban kasa.

Daga cikin wadannan gwamnoni har da wadanda zuwa 2023 ba su kammala wa’adinsu ba. Amma magoya baya suna zuga su cewa su jarraba sa’ar shiga Aso Villa.

Wadannan gwamnonin jihohi sun hada da na jam’iyyar PDP da kuma wasu na APC mai mulki:

Legit.ng Hausa ta tattara wadannan gwamnoni, babu mamaki a karonsu ba su da niyyar neman shugaban kasa, watakila kuma akwai wasu da bamu ambata a nan ba:

Su wanene Gwamnonin nan?

KU KARANTA: Mutane suna so Yahaya Bello ya yi takara idan Buhari zai sauka

1. Aminu Waziru Tambuwal

Akwai alamu masu karfi da ke nuna gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya na sha’awar tsaya wa takarar shugaban kasa a 2023, ya nemi tikiti a PDP a 2019.

Zuwa 2023, tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar ya kammala wa’adinsa. Aminu Tambuwal mai shekara 55 a Duniya shi ne shugaban gwamnonin PDP.

2. Babagana Umara Zulum

Wasu suna zuga gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno a kan cewa ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa a APC a 2023, duk da cewa ya na da sauran wa’adi.

Kwanakin baya aka ga hotunan neman takarar Farfesa Babagana Umara Zulum da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, suna yawo a yankin jihar Gombe.

3. Bala Mohammed

Tun kwanakin baya aka ji cewa wasu sun fara yin kira ga gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya shiga tseren takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Da abin ya yi yawa, tsohon Ministan birnin tarayyar ya fito ya yi magana a makon nan, ya ce bai riga ya yanke hukunci kan batun tsayawa takarar shugabancin kasa ba tukun.

4. Seyi Makinde

Ba a dade da hawan Seyi Makinde kujerar gwamnan jihar Oyo ba, wasu su ka fara rokon shi ya nemi takarar shugaban kasa idan an zo yin zaben 2023 a karkashin PDP.

Injiniya Seyi Makinde ya ciri tuta domin shi kadai ne gwamnan jam’iyyar hamayya a yankin kudancin Najeriya. Makinde ya na da damar ya nemi tazarce har zuwa 2027.

KU KARANTA: Okorocha, Umahi da ‘Yan siyasan Ibo 4 da su ke hangen 2023

5. Nyesom Wike

Tun ba yau ba ake rade-radin cewa Gwmanan jihar Ribas Nyesom Wike ya na harin zama shugaban Najeriya. Sai dai Wike, ya ce shi sam bai da burin rike kasar nan.

Da yake magana kwanaki saboda yawan jita-jita da ake yi, gwamnan yace idan yana da shirin tsaya wa takara, babu wanda ya isa ya taka masa burki a jam'iyyarsa ta PDP.

6. David Umahi

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bar jam’iyyar PDP, ya koma APC kwanaki. Tun lokacin aka ji manyan jihar Ebonyi su na kiran a ba shi tikitin neman Shugaban kasa.

Jim kadan bayan gwamnan ya sauya-sheka, sai fadar shugaban kasa tace Dave Umahi zai iya yin takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar APC a zabe mai zuwa na 2023.

7. Nasir El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya na cikin wadanda magoya baya ke roko ya shiga neman takarar kujerar shugaban kasa a APC, duk da bai nuna sha’awa ba.

Yahaya Bello
Gwamna Yahaya Bello Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 2023: Matasa su na so Wike ya fito takarar Shugaban kasa

8. Rotimi Akeredolu

Wani gwamna daga kudancin Najeriya da ake ganin zai iya neman tikitin takarar shugaban kasa a 2023 shi ne gwamnan Ondo, sai dai ba zai sauka daga mulki ba sai a 2024.

9. Kayode Fayemi

Masu hasashen da fashin bakin siyasa suna ganin Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya na cikin wadanda da gaske za su nemi tikitin APC a zaben shugaban kasa mai zuwa.

10. Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi ya nuna alamu sau da yawa da ke tabbatar da ya na son ya zama magajin Muhammadu Buhari. Yahaya Bello ya na ganin shi ne zai tsaya wa matasa takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng