Fadar shugaban kasa tace Dave Umahi zai iya yin takarar shugaban ƙasa a 2023

Fadar shugaban kasa tace Dave Umahi zai iya yin takarar shugaban ƙasa a 2023

- Mai magana da yawun Shugaba Buhari, Femi Adesina ya ce Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi zai iya takarar shugaban ƙasa a 2023

- Kakakin Shugaban ƙasar ya ce jam'iyyar APC bata fitar da tsarin karba karba ba don haka Umahi yana iya neman duk kujerar da ya ke so

- Femi Adesina ya ce abinda kawai ake ɓukata shine ɗan takarar da masu zabe za suyi na'am da shi su kada masa kuri'a

Femi Adesina, Mai bada shawara na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan kafafen watsa labarai ya ce Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi na iya takarar shugabancin ƙasa a 2023.

Kakakin Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a ranar Juma'a mai laƙabin 'Dave Umahi's Heart of Lion'.

Fadar shugaban kasa tace Dave Umahi zai iya yin takarar shugaban ƙasa a 2023
Fadar shugaban kasa tace Dave Umahi zai iya yin takarar shugaban ƙasa a 2023. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yaki da ta'addanci: Shugabannin kudu sun soki rage makamin da aka yi wa Janar Adeniyi

Ya rubuta cewa a halin yanzu jam'iyyar APC bata fitar da tsarin karɓa-karɓa ba ɗon haka Umahi nada damar takarar ko wane kujerar gwamnati idan har yana da magoya bayan da za su mara masa baya ya kai ga nasara.

A baya bayan nan ne gwamnan na Ebonyi ya fice daga PDP ya koma APC.

Kakakin Shugaban ƙasar ya rubuta cewa "tun lokacin da Umahi ke PDP, baya ɓoye ƙauna da girmamawar da ya ke yi wa Buhari duk da cewa ba jam'iyyarsu ɗaya ba. Kuma shima Buhari na ƙaunarsa. Misali, Ebonyi ce jihar da Buhari ya fara kai ziyarar aiki ya kwana. Umahi na PDP amma zuciyarsa na APC."

Kakakin Shugaban ƙasar ya cigaba da cewa Umahi ya nuna jarumtar na ɗaukan matakin ficewa daga PDP ya koma APC.

KU KARANTA: Tambuwal zai kirkiri Hisbah a jihar Sokoto

Adesina ya shawarci ƴan siyasar kudancin ƙasar su gyara siyasar su idan har suna son jin ƙamshin shugabancin ƙasa.

Jam'iyyar ta APC ta bawa Umahi da Yakubu Dogara damar tsayawa takara duk da cewa ba su daɗe da shigowa jam'iyyar ba.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel