Shugabancin kasa a 2023: Gwamnan Bauchi yace yana tuntubar masu ruwa da tsaki

Shugabancin kasa a 2023: Gwamnan Bauchi yace yana tuntubar masu ruwa da tsaki

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce bai riga ya yanke hukunci kan tsayawa takarar shugabancin kasa ba a 2023
  • Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da wasu kungiyoyi biyu na matasa a arewa suka mika masa wasikar bukatan hakan
  • Gwamnan yace a bashi nan da makonni biyu zuwa uku bayan ya gama ganawa da tattaunawa zai sanar da matsayarsa

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci wata kungiyar siyasa da kungiyar shugabannin matasa ta arewa, da su bashi makonni uku domin tattaunawa tare da yanke shawarar ko zai tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Laraba lokacin da aka gabatar masa da wasikar bukatarsa da ya tsaya takarar shugabancin kasa, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Bayan majalisa ta tabbatar da shi, COAS Yahaya ya sanar da muhimmin albishir ga sojin Najeriya

Shugabancin kasa a 2023: Gwamnan Bauchi yace yana tuntubar masu ruwa da tsaki
Shugabancin kasa a 2023: Gwamnan Bauchi yace yana tuntubar masu ruwa da tsaki. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Jami'ar Kaduna ta koma karatu, ta bukaci iyaye su sa hannu kan wasu takardun alkawari

Mambobin NYLF da suka samu jagorancin shugabansu na kasa Elliot Afiyo, sun gana da gwamnan ne a gidan gwamnatin jihar Bauchi, Daily Trust ta ruwaito.

"Ba zan baku ansa a yanzu ba. Dole ne ya zama in samu tattaunawa da dukkan sassan siyasata kafin in bayyana matsayata.

“Na yi dogaro da Allah da kuma bangaren siyasata. Ku bani nan da makonni biyu zuwa uku sannan in baku ansa takamaimai.

"Ni dan siyasa ne da ya taso daga tsatso mai kyau tun daga aikin gwamnati zuwa siyasa. Allah yayi min baiwa ni da iyalina kuma don haka ba sai na dinga fafutuka kan komai ba a rayuwata. A yanzu ba zan iya cewa eh ba kan bukatarku.

"Ni ne dan siyasa da aka fi farauta tare da tozartawa a kasar nan, tun a 2007 lokacin da na kayar da gwamna mai barin gado inda na zama sanatan Bauchi ta kudu, har zuwa lokacin da na zama ministan Abuja, na cigaba da samun abokan hamayya."

A wani labari na daban, bayan shekaru tara da majalisar wakilai ta rincabe da bincike kan wata damfarar tallafin man fetur, shugaban kwamitin wucin-gadi na wancan lokacin, Farouk Lawan, an yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari kan karbar cin hanci daga biloniya Femi Otedola, mamallakin daya daga cikin kamfanonin da ake bincika.

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Apo wacce ta samu shugabancin mai shari'a Angela Otaluka a ranar Talata, ta kama Lawan da laifuka uku da ake zarginsa dasu tun a 2012, Daily Trust ta wallafa.

Wasu majiyoyi kusa da tsohon dan majalisar sun ce an tasa keyarsa zuwa gidan yarin dake Kuje a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: