Okorocha, Umahi da ‘Yan siyasan Ibo 4 da su ke hangen kujerar Shugaban Najeriya a 2023

Okorocha, Umahi da ‘Yan siyasan Ibo 4 da su ke hangen kujerar Shugaban Najeriya a 2023

- Akwai ‘Yan siyasar Kudu maso gabas da za su nemi takarar Shugaban kasa 2023

- Alamu na nuna cewa Gwamna David Umahi zai so ya yi takaran a jam’iyyar APC

- Masu hasashen siyasa su na ganin ya kamata mulki ya koma Kudancin Najeriya

Saura watanni kusan 20 a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya. Daily Trust ta fara hasashen yadda babban zaben zai kasance a 2023.

Wasu su na da ra’ayin lokaci ya yi da mutumin kudu maso gabas zai zama shugaban kasa, ganin cewa tun 1999 babu Ibon da ya samu shugabanci.

Ga wasu daga cikin ‘yan siyasar da watakila za su nemi takara a karkashin jam’iyyar APC:

KU KARANTA: Okorocha ya ce zai lashe zaben kujerar Shugaban kasa a 2023

1. Dave Umahi

Kwanakin baya Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Tun da ya na da mulki a hannu, wannan zai taimaka masa wajen yakin neman zabe.

Inda matsalar ta ke shi ne Dave Umahi sabon-shiga ne a APC, ba dole ba ne ya san kan jam’iyyar.

2. Rochas Okorocha

Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya na cikin wadanda ba su boye nufinsu ba. Sanatan mai-ci ya dade ya na harin zama shugaban kasa, kuma zai sake jarraba sa’arsa a zabe mai zuwa.

Okorocha zai iya fuskantar matsala tun a gida daga gwamnan jiharsa, Hope Uzodinma. Bayan haka hukumar EFCC ta taso jigon na jam’iyyar APC a gaba, hakan zai iya kawo masa cikas.

KU KARANTA: El-Rufai: Gwamnonin jihohi sun yarda a murkushe ‘Yan bindiga

Okorocha, Umahi da ‘Yan siyasan Ibo 4 da su ke hangen kujerar Shugaban Najeriya a 2023
Okorocha ya na son zama shugaban kasa
Asali: Twitter

3. Orji Uzor Kalu

Orji Uzor Kalu ya na cikin fitattun ‘yan siyasar Kudu maso gabas da su ke neman shugabancin Najeriya. Kamar Rochas Okorocha, ya yi gwamna, kuma ya na majalisar dattawa a yanzu.

Babbar matsalar Sanata Orji Uzor Kalu ita ce an kama shi da laifi har ya yi zaman gidan yari.

4. Ken Nnamani

Wani ‘dan siyasar da ake tunanin zai nemi wannan kujera sun hada da tsohon mataimakin shugaban majalisar datttawan Najeriya, Ken Nnamani wanda ya fito daga Enugu.

A shekarar nan Sanata Ken Nnamani zai cika shekara 73, wasu na ganin shekaru sun yi masa nisa.

Masu fashin bakin siyasa su na ganin harin takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ta sa gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya dawo jam’iyyar APC.

David Umahi, ya yi karin bayani game da abin da ya sa ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC. A cewarsa shugaba Muhammadu Buhari ya jawo sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel