Ba zan yi takarar shugaban kasa ba a 2023 - Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce sam ba wata sharar hanya da ya ke ta neman fitowa takarar shugabancin Najeriya a babban zaben kasa na shekarar 2023.
Wike ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai na Gidan Talabijin din Arise a ranar Lahadi kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.
Bayanin Wike ya zo ne a daidai lokacin da ake yada jita-jitar cewa ya fara nuna kwadayi da hangen kujerar fadar shugaban kasar Najeriya.
Gwamnan na jam'iyyar PDP yayin musanta wannan zargi, ya sanar da cewa za a yi gaggawa muddin tun a yanzu aka fara tunani kan siyasar 2023.
Gwamnan ya misalta wannan jita-jita da ake danganta shi ta burin zama shugaban kasa a matsayin wani abu da zai iya dauke masa hankali.
Ya ce a halin yanzu, babu abin da ya sa a gaba tare da mayar da hankalinsa a kai face tabbatar da cewa al'ummar jihar Ribas sun kwankwadi romon dimokuradiyya a karkashin jagorancinsa.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamna Wike ya nuna farin cikinsa a kan yadda a halin yanzu jam' iyyar APC mai mulki ta tsinci kanta cikin rikici.
Ya ce yana farin cikin halin da jam'iyyar ta tsinci kanta da kuma yadda takwaransa na jihar Edo, Godwin Obasekiya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa ta su ta PDP.
KARANTA KUMA: FBI ta nemi taimakon kama wasu 'yan Najeriya da suka aikata zambar $6m
Wike ya ce ba zai taba yi wa jam'iyyar APC fatan ta daina kura-kurai da shiga cikin matsala domin kuwa a cewarsa hakan shi zai ba wa PDP damar karbe mulki a 2023.
"Ina farin ciki a kan rikicin APC. Ba matsala ta bace don haka babu bukatar su samu hadin kai," inji Wike."
"Idan za ku tuna mun samu rikici a zamanin da Ali Modu Sheriff ke jagorancin jam'iyyarmu, kuma APC ta yi murna da hakan. Ina fatan rikicin ya ci gaba."
"Ina fatan jam'iyyata ta samu mulkin kasar nan. Saboda hakan bana fatan rikicin APC ya wuce. Ina fatan su ci gaba da kura-kurai sannan jam'iyyata ta ci gaba da bunkasa."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng