Zaben 2023: Dinbin mutane suna so Yahaya Bello ya yi takara idan Shugaba Buhari zai sauka

Zaben 2023: Dinbin mutane suna so Yahaya Bello ya yi takara idan Shugaba Buhari zai sauka

- Wasu magoya bayan Gwamna Yahaya Bello sun gudanar da taro a Ibadan

- Masoyan gwamnan jihar Kogi sun yi kira gare shi ya yi takara a zaben 2023

- Gwamna Bello ya turo wani wakili da ya halarci taron, ya nuna jin dadinsa

Masoyan Yahaya Bello a karkashin 'South-West Benefit Conference and a non-partisan group, Afenifere for Collective Transformation' sun shirya taro a jiya.

Wasu daga cikin Magoya bayan gwamnan na jihar Kogi ya nemi takarar shugaban kasa a 2023 sun shirya wannan taron wayar da kai a garin Ibadan, jihar Oyo.

Jaridar Daily Trust ta ce an yi wannan taro ne a wani otel da ke Mokola, Ibadan, wanda dinbin magoya bayan gwamnan jihar Kogi daga jihohi shida suka halarta.

KU KARANTA: Ana saura kwana 150 ayi zaben Gwamna, an cinnawa INEC wuta

Magoya bayan Gwamnan sun fito ne daga Legas, Oyo, Ondo, Ogun, Osun, Ogun, Ekiti, Kogi da Kwara.

An yi wa wannan taro take da: “Matasa ke da mulki”, inda masoyan Yahaya Bello suka fito, suna kira ga gwamnan Kogi ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Gwamna Bello ya gode wa yadda magoyan na sa suke bada goyon baya, ya ce ya samu nasara a jihar Kogi ne saboda rashin nuna banbamcin kabilanci da addini.

Darekta-Janar na sha’anin nazari da cigaba, kuma mai rubuta wa gwamnan jihar Kogi, jawabinsa, Moses Okezie-Okafor, shi ne ya wakilci gwamnan a wajen taron.

Zaben 2023: Dinbin mutane suna so Yahaya Bello ya yi takara idan Shugaba Buhari zai sauka
Gwamna Yahaya Bello Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Kalubale ya na jiran Buhari wajen nada shugaban hafsun sojan kasa

Barista Moses Okezie-Okafor yace idan ya samu mulkin Najeriya, zai magance matsalolin tsaro.

A madadin mai girma gwamnan jihar Kogi, Moses Okezie-Okafor, yace idan damar rike madafan iko ta shigo hannunsa, zai yi bakin kokarinsa na tsare al’umma.

The Cable ta ce gwamna Bello yana cikin wadanda suke harin kujerar shugaban kasa a karksashin APC, har ya na ganin Bola Tinubu zai mara masa baya.

Kwanakin baya wata kungiyar siyasa dake goyon bayan Gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello ta ce gwaninta ne zai iya magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Kungiyar tace Yahaya Bello zai cin ma wannan ne ta hanyar yin amfani da dabarun da ya yi aiki da su wajen kiyaye jiharsa ta Kogi lafiya a shekarun da yayi a mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel