Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

- Gwamnan Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 dake tafe

- Wike yace idan yana da muradin tsayawa takara a jam'iyyarsa ta PDP, babu wanda ya isa ya dakatar dashi

- Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da yake martani ga kalaman da tsohon gwamnan Neja yayi a kansa satin da ya gabata

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: El-Rufa'I Yayi Magana Kan Sabon Shugaban Sojin Ƙasa Janar Yahaya Faruk, Yace Mutum Ne Mai Juriya

Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da yake maida martani ga tsohon gwamnan jihar Neja, Dr. Babangida Aliyu, kamar yadda guardian ta ruwaito.

Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023
Gwamna Wike Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023 Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Da yake jawabi, Wike yace: "Idan wani na da muradin tsayawa takarar shugaban ƙasa zaka ganshi ya kasa zama wuri ɗaya, daga nan zuwa can."

"Shin ka taɓa gani na ina biye-biye? Na ƙalubalance su baki ɗaya, idan inason neman kujerar shugaban ƙasa, ba wanda ya isa ya hana ni."

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Mun Cafke Masu Aikata Manyan Laifuka Sama da 1,000 Cikin Wata Ɗaya Kacal, IGP

Yayin da Wike yake magana kan takarar shugaban ƙasa, ya ƙara da cewa:

"Ba su da ƙarfin guiwa, wani lokacin sai kaji ance yana neman kujerar mataimaki, shin ka taɓa jin wani na neman takarar mataimaki? Wani lokacin suna ƙalubalantar kan su da kan su."

"Aliyu ya fito ya faɗi cewa da shi aka kawar da tsohon shugaban ƙasa Goddluck Jonathan, amma kun ɗauke shi kun sa shi cikin manyan masu yanke hukunci a jam'iyya."

A wani labarin Kuma Minista Tayi Magana Kan Shirin N-Power, Tace an Biya Dukkan Ma’aikata Haƙkinsu.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu mai binta bashi daga cikin ma'aikatan Npower da suka gama aiki

Ministar ma'aikatar jin kai da walwala, Sadiya Farouk, itace ta bayyana haka, tace an biya ko wane ma'aikaci haƙƙinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel