Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe

Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe

- Da alamu Adams Oshiomole da Gwamna Zulum za su fito takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC

- An gano hotunan 'yan siyasar biyu a jihar Gombe, in da suke yi al'ummar musulmi barka da sallah

- Wata kungiyar kishin arewa ne ta dauki nauyin bugawa da yada hotunan a fadin jihar ta Gombe

An ga fostoci dauke da hotunan Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum tare da tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomole dake yi wa al'ummar musulmi barka da zagayowar karamar sallah.

Wakilin Legit.ng Hausa ya gano hotunan a wurare da dama a birnin Gombe, a ranar karamar wanda yayi daidai da 13 ga watan Mayu, 2021.

Hotunan na nuni da alamun cewa, Oshiomole da Zulum za su tsaya takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na shekarar 2023 a karkashin jam'iyyar APC kamar yadda fostar ta nuna.

KU KARANTA: Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge ’Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano

Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe
Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An rubuta "Barka da Sallah OZ2023, Oshiomole/Zulum" a saman fostar, wanda ke nuna karara akwai wani abu da ake hange nan gaba a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

A kasan hotunan, an rubuta sunan kungiyar da ta dauki nauyin watsa hotunan.

Kungiyar Hadin Gwiwar Masu Kishin Arewa Don Samar da Adalci, Daidaito, Zaman Lafiya da Hadin kan Najeriya ce ta dauki nauyin bugawa tare da watsa hotunan.

Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe
Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Gwamna Zulum na daya daga cikin gwamnonin da 'yan Najeriya ke yaba mulkinsu, musamman duba da yadda ya ke jajircewa wajen kwakwaf a fadin jiharsa.

KU KARANTA: Bayan Ruwan Sama, Tsawa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu Sama da 12 a Delta

A wani labarin, Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a ranar Laraba da yamma, ya kori kwamishinoni 20 daga cikin kwamishinonin sa 28.

Kwamishinoni takwas da sanarwar ba ta shafa ba sun kasance daga ma'aikatun lafiya, matasa da wasanni, yawon bude ido, yada labarai da dabaru, al'amuran mata, ayyuka, kudi da fasaha.

Jaridar Punch a baya ta ruwaito cewa gwamnan yayi zargin makwanni biyu da suka gabata cewa wasu daga cikin wadanda ya nada suna zagon kasa ga gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel