2023: Matasa 5,000 sun nemi PDP ta sanya Wike a takarar zaben Shugaban kasa

2023: Matasa 5,000 sun nemi PDP ta sanya Wike a takarar zaben Shugaban kasa

- Matasan Kudu maso Yamma da dama sun zabi Gwamna Nyesom Wike a matsayin dan PDP mafi cancanta da zai iya karawa da APC a zaben shugaban kasa na 2023

- A yanzu haka, matasan PDP 5,000 sun nuna goyon bayansu ga gwamnan na Ribas dari bisa dari

- Matasan na PDP sun yi imanin cewa Wike zai yi wa APC zarra a yayin zaben shugaban kasa na 2023

Akalla matasan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 5000 daga kudu maso yamma ne suka nuna goyon bayansu ga Gwamna Nyesom Wike gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Matasan sun ce da Gwamna Wike a matsayin abokin takara, PDP na da kyakkyawar dama fiye da kullun don tsige jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga sama a siyasar kasa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Sun yi ikirarin cewa ba tare da ja ba, gwamnan na Ribas zai iya karawa da kowacce jam’iyya duba ga gudunmawar da yake bayarwa a harkokin PDP da tsarin shugabancinsa a jihar Ribas.

2023: Matasan kudu maso yamma 5,000 sun nemi PDP ta sanya Wike a takarar zaben Shugaban kasa
2023: Matasan kudu maso yamma 5,000 sun nemi PDP ta sanya Wike a takarar zaben Shugaban kasa Hoto: Governor Nyesom Wike
Source: Facebook

KU KARANTA KUMA: An samu rudani yayinda El-Rufai da ma’aikata suka ba da umarni daban-daban kan rufe makarantu

Jagoran kungiyar matasan, Kwamared Akeem Adebomojo, a cikin wata sanarwa ya shawarci PDP da ta tsayar da wasu gagaruman mutane tare da Wike don samun karfi a yayin zaben.

Adebomojo ya ce:

“Muna kira ga babbar jam’iyyarmu da ta tabbatar da ganin cewar an tsayar da Gwamna Nyesom Wike a matsayin dan takarar Mataimakin Shugaban kasa kuma abokin takara ga duk wanda ya zama dan takarar Shugaban kasa a zaben 2023.

“Mun kai ga wannan matsayar ne, bayan bin diddigin abubuwan da suka haifar da faduwar jam’iyyar a zaben Shugaban Kasa na 2019, duk da guguwar gazawar gwamnatin Buhari da APC.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Nigeria ta ragargaji mayakan Boko Haram a wani arangama

"Har ila yau, babu tantama cewa Gwamna Wike ya yi rawar gani a Jihar Ribas ta yadda zai iya lallasa APC ."

A wani labarin, akwai fargaba a tsakanin mambobin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) yayin da alamu suka nuna cewa nan ba da jimawa ba jam'iyyar za ta bayyana matsayarta kan batun raba tikitin takarar shugaban kasa a 2023.

Jaridar Sun ta rahoto cewa wannan na zuwa ne yayin da aka shirya kwamitin sake duba babban zaben jam’iyyar adawar ta 2019 don gabatar da rahotonta a ranar Laraba, 17 ga watan Maris.

Legit.ng ta tattaro cewa kwamitin, wanda aka kaddamar a shekarar 2020, karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel