Dan addinin gargajiya mai shekara 78 ya Musulunta a Oyo

Dan addinin gargajiya mai shekara 78 ya Musulunta a Oyo

  • Ezekiel Adekunle Eleede, mai shekara 78 da ke bin addinin gargajiya a Jihar Oyo ya sanar da Musuluntarsa
  • Dattijon ya ce ya yi bautar gumaka na tsawon shekaru kafin daga bisani ya yanke shawarar karbar Musulunci
  • Eleede, wanda a yanzu yake amsa sunan Abdusalam Adekunle, ya ce ya gamsu cewa Musulunci shi ne addinin Allah

A wani abin mamaki wani dattijo mai shekara 78 mabiyin addinin gargajiya mai suna Ezekiel Adekunle Eleede, a garin Okeho da ke Jihar Oyo ya yi watsi da bautar gumaka inda ya karbi addinin Musulunci.

Wakilin kafar labaran Legit.ng a Jihar Oyo, Imran Khalid, ya bada rahoton cewa dattijon wanda shi ne jagoran masu bautar gumaka da mafarautan kauyen da yake zama na tsawon shekara 15 ya yi watsi da dukkanin gumakan jim kadan bayan da ya amshi addinin Musuluncin.

Tsohon mai bautar gumakan bayan ya shiga Musuluncin, sanannen malamin addinin Msulunci a jihar, Alhaji Daud Awayewaserere ya sauya masa suna zuwa Abdussalam Adekunle, bayan da ya jaddada Allah daya ne.

Da yake magana da kafar Legit.ng ya bayyana cewa shi da kashin kansa ne ya amince da ya shiga Musuluncin, bayan ya lura cewa gumakan da ya yi ta bauta wan a tsawon shekara 15 ba su tsinana wa rayuwarsa da na wadanda suke zama tare wani abin arziki ba.

‘’Ina murnar zama Musulmi. Ban taba zuwa kowane coci ko masallaci ba tunda aka haife ni,’’ a cewar Abdsalam.

KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997

Dan addinin gargajiya mai shekara 78 ya Musulunta a Oyo
Dan addinin gargajiya mai shekara 78 ya Musulunta a Oyo
Asali: Original

KU KARANTA: Waiwayen Tarihi: Gagarumar gobarar da ta faru a Mina a Hajjin 1997

Ya kara da cewa ya gane cewa addinin gaskiya a wajen Allah sannan ba zai taba daina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

Ya ce ya fara jin sha’awar addinin Musulunci bayan da abokansa a addinin suka yi ta nuna masa addinin Musulunci ya fi bautar gumaka nesa ba kusa ba.

Babu abinda gumaka suka tsinana min

Dattijon ya nunar da cewa duk da yadda ya yi ta bautar gumakan, ba su iya yaye masa matsalolin ciwon kafa da na ido da yake fama da su ba.

Abdsalam ya ce tun bayan da ya Musuluntan, sai rayuwa ta fara sauya masa sannan ko abincin da yake ci yana samun sa cikin sauki lura da yadda bayin Allah ke kai masa sadaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel