Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in Soja

Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in Soja

  • Kakin Soji ya ce sai an yi amfani da dabarbaru maimakon amfani da karfin tuwo domin shawo kan kalubalen tsaro
  • Kafofin yada labarai nada matukar muhimmanci a yaki da matsalolin tsaron, a cewarsa
  • Ya bada tabbacin aiki tukuru domin inganta dangantakar sojojin da jama’a

Wani jami’in sojin Najeriya a ranar Laraba ya bayyana cewa amfani da bindiga kadai ba zai iya kawo karshen barazanar tsaron da ake fama da shi a fadin kasar nan ba.

Kakakin rundunar Birgediya Janal Onyema Nwachukwu, wanda ya bayyana hakan, ya ce kalubalen tsaron da ake fuskanta a bangarori daban daban na bukatar amfani da wasu dabarbaru na daban domin shawo kansu.

Da yake magana yayin karbar ragamar Daraktan Hulda da na Jama'a na sojin kasa a Hedkwatar Sojojin da ke Abuja, Janal Nwachukwu ya ce:

“Ku ba ni dama, an lura kuma hujja ce tabbatacciya, cewa takobi ko bindiga, ba za su iya zama maganin kalubalen tsaro masu sarkakiya wadanda suka addabi duniyar nan a yau.
“Don haka, lallai ne in ambata cewa wadannan kalubalen tsaron na bukatar amfani da dabarbaru daban daban tare da hadin kan masu ruwa da tsaki a batun harkar tsaro, wanda kafafen yada labarai na da matukar muhimmanci a ciki.
"Domin shawo kan wadannan kalubale, dole ne rundunar sojin kasa da kafofin yada labarai su zama abokan hadin gwiwa domin shawo kan wannan barazanar tsaro da zimmar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da muke matukar bukata a matsayinmu na mutane da al'umma."

KU KARANTA: Alheri kan alheri: Ma’aurata ’yan Najeriya sun samu ’yan biyu shekara 21 suna jiran haihuwa

Kakakin soja
Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in soja Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

KU DUBA: Ana mini barazanar kisa, Shugaban Hukumar EFCC Abdulrashid Bawa

Nwachukwu ya zama sabon Kakin Soji

An nada Janal Nwachukwu mukamin mai magana da yawun rundunar a cikin garambawul da aka yi da a mukaman rundunar sojan kasa na Najeriya, bayan nadin Manjo-Janal Farouk Yahaya a matsayin Shugaban Hafsan sojan kasa wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Ya haye mukamin ne daga hannun Birgediya Janal Mohammed Yerima.

Janar Nwachukwu ya ce yana sane da nauyin da ke kansa na tsara ayyukan rundunar tare da kokarin karfafa dangantaka da goyon baya ga rundunar sojin kasan.

Da yake yaba wa Babban Hafsan Sojin Kasan saboda yadda ya ga cancantar ya nada shi a wannan mukamin, Janal Nwachukwu, ya yi alkawarin inganta kimar rundunar sojin kasan Najeriya.

A bangare guda, wasu masu tayar da kayar baya da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne sun mamaye wani sansanin sojoji a kudancin jihar Borno a ranar Talata sannan suka kwashe makamai bayan wani kazamin artabu da sojojin, in ji rahoton Daily Trust.

An gano cewa mayakan sun zo cikin motoci kusan 10 domin yin kawanya ga rundunar da aka kafa a kauyen Kwamdi, da ke karamar hukumar Damboa da yammacin ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel