Abdulrasheed Bawa: EFCC ta karbo $100m a hannun tsohon kamfanin Atiku, Intels

Abdulrasheed Bawa: EFCC ta karbo $100m a hannun tsohon kamfanin Atiku, Intels

  • Abdulrasheed Bawa ya ce EFCC ta taimakawa NPA wurin karbo wasu kudi
  • Kamfanin Intels ya fito da wasu kudi $100m da ya kamata ya ba Gwamnati
  • Shugaban EFCC ya bayyana wannan a cikin irin nasarorin da ya samu a ofis

Shugaban EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa, Abdulrasheed Bawa, ya ce sun yi nasarar karbo wasu kudi har $100m a madadin NPA.

Jaridar The Cable ta rahoto Abdulrasheed Bawa ya na cewa sun karbo wadannan makudan kudi a hannun kamfanin Integrated Logistics Services (INTELS).

Bawa ya ce ba gwamnatin tarayya kadai hukumar EFCC ta ke yi wa aiki, ya ce suna karbo hakkin duk wani da aka yi wa satar kudi ko wata dukiya a Najeriya.

KU KARANTA: Za mu yi maganin masu hana kasa cigaba - EFCC

INTELS sun dawo da kusan Naira biliyan 50

A irin haka ne hukumar EFCC ta karbo adadin da ya kai fam miliyan 100 na ma’aikatar NPA a hannun kamfanin INTELS da wasu kudin Najeriya ke hannunsa.

Kamar yadda The Nation ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, shugaban EFCC ya ce wadannan kudi suna cikin rarar da ya kamata INTEL ta sa a asusun gwamnati.

An yi wannan ne kafin a 2017, Abubakar Malami ya soke yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta shiga da kamfanin, Ministan ya ce yarjejeniyar ta saba dokar kasa.

Abdulrasheed Bawa yake cewa:

Mr Abdulrasheed Bawa
Abdulrasheed Bawa Hoto: www.arise.tv
Asali: Facebook

KU KARANTA: Atiku ya saida hannun jarinsa a Intel saboda tsangwamar gwamnati

“Yan kwanakin bayan nan, mun karbo wa hukumar NOA $100m, an maida kudin zuwa cikin asusun NPA, amma a sanadiyyar kokarinmu ne aka yi haka.”
“Ba zan rubuta cewa mun karbo wa NPA wadannan kudi ba? Za a ga kudin a cikin asusun hukumar EFCC da ke hannun babban bankin kasa na CBN? A’a!"

Bawa ya ce ba wai an maida wadannan kudi da aka karbo kai-tsaye zuwa asusun EFCC ba ne.

Sauran nasarorin da aka samu

"Mun karbo N6bn, fiye da $161m, sama da £13,000, €1,730, 200 Canadian dollars, CFA 373,000, ¥8,430. "
"Mun karbo Da gidaje 30, daddamu daya, na’urorin lantaki 13, gona daya, kamfani daya, babur biyu, gidan mai daya, da motoci 32."

Abdulrasheed Bawa ya yi duk wannan bayani yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa, ya na bayanin nasarorin da ya samu a cikin kwana 100.

A jiyan ne kuma aka ji cewa tun da an janye yajin-aiki a kotu, EFCC za ta gabatar da kara 800 a kotu domin a hukunta masu satar dukiyar gwaamnati da damfarar mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel