Mai dakin Shugaba Buhari ta yi taro da Matan Hafsun Sojoji, ta ba Gwamnati shawarwari

Mai dakin Shugaba Buhari ta yi taro da Matan Hafsun Sojoji, ta ba Gwamnati shawarwari

  • Aisha Buhari ta gana da matan Shugabannin tsaro na kasa a birnin tarayya
  • Matan Hafsoshin sojoji, IGP, Shugaban DSS sun halarci wannan zama a jiya
  • Matar Shugaban kasar ta ba iyalan manyan kasar da gwamnati shawarwari

Uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ta bukaci hukuma ta yi abin da ya kamata na ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro.

Jaridar Punch ta ce Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta bada shawarar a dauki sababbin jami’ai wadanda za su taimaka wajen yakar masu tada kafar baya.

Matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi wannan kira ne a lokacin da ta zauna da matan shugabannin hafsoshin tsaro na kasa a fadar Aso Villa jiya.

KU KARANTA: Ban isa in yi waje da Hadiza daga ofis ba - Amaechi

Mai taimakawa matar shugaban kasar wajen sha’anin yada labarai da hulda jama’a, Aliyu Abdullahi, ya fitar da wannan jawabi a Abuja a ranar Litinin.

Mai magana da yawun Aisha Buhari ya yi jawabin take da ‘Aisha Buhari charges wives of service chiefs.’

Uwargidar ta yi magana a kan abin da ya shafi rawar da mata za su taka wajen cigaban kasa, ta ce ya kamata su ba mazajensu gudumuwar kawo zaman lafiya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa a jawabinta, Buhari ta yi kira ga iyalan matan manyan su rike alaka mai kyau da kowa a lokacin dadi da rashinsa.

KU KARANTA: Sabon hafsun sojojin kasa ya bayyana a gaban 'Yan Majalisa

Aisha Buhari da Matan Hafsun Sojoji
Aisha Buhari da Matan Hafsun Sojoji Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

A rika biyan tsofaffin jami’ai hakkinsu

Har ila yau rahoton ya ce Aisha Buhari ta yi amfani da wannan dama ta yi kira ga hukumomi su rika biyan fanshon tsofaffin sojoji da su kayi ritaya a kan kari.

Hakan zai zaburar da sauran jami’an da suke aiki a halin yanzu, a cewar Buhari mai shekara 50.

An yabawa Aisha Buhari

Mai dakin hafsun tsaor na kasa, Victoria Irabor ta yi jawabi, inda ta wakilci sauran takwarorinta. Irabor ta yaba wa kokari da gudumuwar da Buhari take ba sojoji.

Dazu kun ji cewa Frank Kokori, ya bada labarin yadda aka toshe mukamin da Farfesa Yemi Osinbajo ya ba shi a lokacin da shugaban kasa Buhari bai lafiya.

Tsohon Shugaban NSITF, Frank Kokori, ya ce masu rike da madafan iko ne su ka ki bari a rantsar da shi a kan kujerar, ya ce wasu miyagu ne ke rike da gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel