"Akwai miyagu da ke zagaye da Buhari da sun fi Osinbajo karfin iko, su ke juya gwamnatin nan"

"Akwai miyagu da ke zagaye da Buhari da sun fi Osinbajo karfin iko, su ke juya gwamnatin nan"

  • Frank Kokori ya ce akwai wadanda suke juya gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Cif Frank Kokori ya bada labarin sallamar shi da aka yi daga shugabancin NSITF
  • Dattijon ya ce wasu Hadimai suna amfani da tsufan Buhari, suyi abin da suke so

Fitaccen ‘dan gwagwarmayar ‘yan kwadago kuma dattijo, Frank Kokori, ya bada labarin yadda aka toshe mukamin da Farfesa Yemi Osinbajo ya ba shi.

Jaridar Punch ta rahoto Cif Frank Kokori ya na cewa Yemi Osinbajo ya nada shi a matsayin shugaban NSITF a lokacin da yake rike da kasa a 2017.

Dattijon ya yi bayani cewa mukaddashin shugaban kasa ya ba shi mukami, amma bayan shugaba Muhammadu Buhari ya dawo kasa, sai aka karbe kujerar.

KU KARANTA: Irin shugabanin da ake bukata a kasar nan - Osinbajo

Bayan Kokori ya dade ba tare da an rantsar da shi a matsayin shugaban NSITF ba, sai aka ji Ministan kwadago, Chris Ngife ya bada Austin Enajemo-Isire.

“Buhari yana da iyakarsa, ita ce shekarunsa. Ina tunanin matsalar ita ce wadanda ke tare da shi da ake kira ‘yan fadar shugaban kasa, ko wasu gungun miyagu.”

Kamar yadda Nairaland ta kawo, Frank Kokori ya ce: “Su na amfani da shi, su yi duk abin da suka ga dama da sunansa, sai su ce fadar shugaban kasa ce ta ce.”

“Da aka ba ni kujerar shugaban hukumar NSITF a lokacin Yemi Osinbajo yana rikon kwarya, Buhari ya na dawowa, sai aka ce bai dace a bar ni a nan ba.”

"Akwai miyagu da ke zagaye da Buhari da sun fi Osinbajo iko, suke juya gwamnatin nan"
Cif Frank Kokori Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: PDP ta ce Buhari na neman kashe Najeriya

Kokai yace an saba barin maras gaskiya ya rike wannan mukami mai alhakin kula da fanshon al’umma.

A lokacin da Abba Kyari yake ofis, shugaban kasa da kansa ya fadawa Kokari zai shiga ofis, a cewarsa. A karshe sai Minista ya nada abokinsa, Enajemo-Isire.

Buhari ya yi kokari in rike ofishin nan, amma hakan ya gagara, kuma ba za ka taba iya tuntubarsa ba, shi ne shugaban da ya fi kowane wahalar gani a tarihi.”

Ya ce: “Sun maida Osinbajo wanda yana da kwakwala a gefe, bai iya komai ba. Wasu ne ke juya kasar, ya zama shugaban ma’aikatar fada ya fi SGF da Osinbajo karfi.”

A ranar Lahadin da ta gabata ne ku ka ji cewa takarar Yahaya Bello ta samu kwarin gwiwa da goyon bayan ya samu goyon tsohon tauraron Super Eagles, Mikel Obi.

Tsohon ‘Dan wasan kungiyar Chelsea, Obi ya ce Bello ne ya cancaci ya jagoranci matasan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng