Karin Bayani: Yan Majalisar Wakilai Sun Tantance Sabon Hafsan Soji, Manjo Janar Farouk Yahaya

Karin Bayani: Yan Majalisar Wakilai Sun Tantance Sabon Hafsan Soji, Manjo Janar Farouk Yahaya

  • Majalisar wakilai ta tarayya ta tantance, shugaban rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya
  • A kwanakin baya, shugaban ƙasa Buhari, ya bayyana naɗin Janar Yahaya a matsayin sabon hafsan sojin ƙasa
  • Janar Yahaya zai gaji tsohon COAS, janar Ibrahim Attahiru, waɓda ya mutu sanadiyyar hatsarin jirgi

Haɗakar kwamitin tsaro da na jami'an sojin ƙasa, sun tantance sabon hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

A ranar Talata da ta gabata, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya karanta wasikar shugaba Buhari ta neman amincewa da Yahaya a matsayin sabon COAS.

KARANTA ANAN: Wani Gwamnan Arewa Ya Ƙaddamar da Sabbin Jami'an Tsaro Na Musamman a Jiharsa

Babajimi Benson, shugaban kwamitin tsaro na majalisar, yace tantance sabon COAS ɗin yazo dai-dai lokacin da Najeriya ke fama da matsaloli daban-daban a ɓangaren tsaro.

Hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Yahaya Ya Isa Majalisa domin tantancewa
Da Ɗuminsa: Sabon Hafsan Sojin Ƙasa, COAS, Farouk Yahaya, Ya Bayyana Gaban Majalisa Domin Tatancewa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa, ya zama wajibi sabon shugaban rundunar sojin ya tabbatar ya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ƙasa ke fam da shi.

Shugaba Buhari ya naɗa Manjo Janar Yahaya a ranar 27 ga watan Mayu domin ya maye gurbin tsohon COAS, Ibrahim Attahiru, wanda ya rasu sanadiyyar hatsarin jirgi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kada Ku Yarda Yan Bindiga Su Kashe ku, Gwamna Ya Gargaɗi Yan Sanda

Janar Yahaya ya faɗawa yan majalisar cewa yana da kwarewar da ake buƙata wajen jagorancin rundunar sojin ƙasa idan suka tabbatar da shi a matsayin COAS.

Yace: "Nayi imani cewa ina da duk abunda ake buƙata da yardar Allah zan jagoranci sojin ƙasa idan aka tabbatar da ni."

"Abinda na zo muku da shi, shine kwarewata da sadaukarwar da nayi a lokacin aiki na har zuwa lokacin da aka naɗa ni a wannan matsayi."

"A shirye nake nayi amfani da dukkan gogewata domin samar da sakamako mai kyau."

Yahaya ya ƙara da cewa zai yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa tsakanin shi da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da birne matsalar tsaro a ƙasar nan.

A wani labarin kuma Fulani Makiyaya Sun Kashe Mutum 2 Tare da Sace Wasu 6 a Enugu da Akwa Ibom

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutum ɗaya tare da sace 5 a jihar Enugu.

Maharan sun nemi iyalan waɗanda abun ya shafa da su biya naira miliyan N10m domin su fanshi yan uwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel