Ba ni da masaniyar na sallami Hadiza Bala Usman daga hukumar NPA inji Rotimi Amaechi

Ba ni da masaniyar na sallami Hadiza Bala Usman daga hukumar NPA inji Rotimi Amaechi

  • Rotimi Amaechi yana ikirarin bai san an dakatar da Hadiza Bala Usman ba
  • Ministan Sufurin ya ce an kawai bukaci Shugabar NPA ta matsa gefe guda ne
  • Amaechi ya ce Shugaban kasa ne kurum yake da iko a kan Shugabar ta NPA

The Cable ta rahoto Ministan harkar sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, ya na cewa bai da labarin an dakatar da Hadiza Bala-Usman daga aiki a hukumar ta NPA.

Babban Ministan na Najeriya ya yi hira ne da gidan talabijin na Arise TV a ranar Litinin, 14 ga watan Yuni, 2021, ya tabo maganar biciken da ake yi a NPA.

Rotimi Amaechi ya ce abin da ya faru shi ne an umarci Hadiza Bala-Usman ta matsa gefe guda ne har zuwa lokacin da kwamiti zai karkare binciken da yake yi.

KU KARANTA: Yadda Bala Usman ta sa aka yi waje da ni a NPA - Sanata

“Ba ni da labarin cewa na dakatar da Hadiza. Ba ni ba ne shugaban kasa, saboda haka ba ni da wannan iko. Wannan hurumin shugaban kasa ne.” inji Amaechi.

Ban da masaniyar an dakatar da Hadiza. Abin da ya faru shi ne, ina zargin an umarce ta da ta matsa gefe domin a bada damar yin binciken da ake yi a NPA.”

Ministan ya yi karin haske, ya ce ana binciken hukumar NPA ne ba wai Hadiza Bala-Usman ba.

Amaechi ya ce: “Muna binciken NPA ne. A karshen bincikenmu, za a tattara rahoto duk a kai wa shugaban kasa, wanda shi ne zai zartar da matakin da za a dauka.”

KU KARANTA: Dalilin sabanin Hadiza Bala Usman da Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi da Shugabar NPA
Rotimi Amaechi da Hadiza Bala-Usman Hoto: www.thenationonlineng.net
Asali: UGC

Har ila yau, Ministan ya ce bai san lokacin da kwamitin da ya kafa zai kammala wannan aiki ba.

“Ba ma’aikatar sufuri ta kasa ke jagorantar binciken ba, ofishin shugaban ma’aikatar gwamnatin tarayya ta kawo mutane shida, ma’aikatar sufuri ta kawo biyar.”

Tsohon gwamnan ya zargi ‘yan jarida da yawan surutu a kan abin da ya faru da shugabar ta NPA.

Dazu ne aka ji tsohon shugaban hukumar NSITF, Cif Frank Kokari ya na cewa akwai wasu masu rike da madafan iko dabam bayan shugaban kasa da mataimakinsa.

Frank Kokari ya ce a lokacin da Muhammadu Buhari bai da lafiya, ya na jinya a waje, an ba shi mukami, amma Buhari na dawowa aka karbe kujerar da karfin tsiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel