Gwamnatin Kaduna ta tabbatar an sace dalibai da dama a harin Kwalejin Nuhu Bamalli

Gwamnatin Kaduna ta tabbatar an sace dalibai da dama a harin Kwalejin Nuhu Bamalli

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da harin da aka kai Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Zaria
  • Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na jihar Kaduna ya ziyarci Kwalejin tare da wasu jami'an gwamnati
  • Sanarwar ta Aruwan ya fitar ta ce kawo yanzu akwai wasu dalibai da ake nema amma ba a gansu ba

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar an sace wasu dalibai a harin da yan bindiga suka kai Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria, Premium Times ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito yadda yan bindigan suka kutsa makarantar ne inda suka sace malamai kuma aka nemi wasu daliban aka rasa.

Samuel Aruwan tare da malamai da daliban Kwalejin Nuhu Bamalli
Kwamishinan tsaro na Kaduna, Samuel Aruwan tare da malamai da daliban Kwalejin Nuhu Bamalli. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Daya daga cikin daliban da ya samu rauni sakamakon harbinsa da bindiga da aka yi ya riga mu gidan gaskiya a ranar Juma'a.

A cewar sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar, har yanzu akwai wasu dalibai da ba a gansu ba.

DUBA WANNAN: A karon farko, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi magana kan haramta Twitter a Nigeria

"Jami'an tsaro sun yi wa gwamnatin jihar Kaduna bayani kan harin da yan bindiga suka kai Kwalejin Kimiyya ta Nuhu Bamalli da ke Zaria, a daren ranar Alhamis.

"A cewar bayanin, yan bindigan sun kutsa gidajen malaman kwalejin suna harbe-harbe. A hakan ne suka harbi dalibai biyu, sunayensu Ahmad Muhammad da Haruna Isyaku Duniya.

"An garzaya da su asibiti don basu kulawa. Ahmad Muhammad ya rasu a safiyar yau. Haruna Isiyaku yana cigaba da jinya.

"Gwamna Nasir El-Rufai ya yi addu'ar Allah ya jikan wanda ya rasu ya kuma yi wa wanda ke jinya fatan samun sauki cikin gaggawa.

"A lokacin hada wannan rahoton, jami'an gwamnati suna tattaunawa da mahukunta makarantar suna nazarin tsaro," a cewar Mr Aruwan.

KU KARANTA: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Wani ma'aikaci a makarantar ya shaidawa Premium Times cewa a yanzu akwai dalibai da dama da ba a gansu ba.

"Dalibai na neman abokan zamasu, har yanzu akwai wadanda ba a gansu ba, kuma wayarsu a kashe, amma ta farko kirar na shiga."

A wani rahoton daban, kun ji cewa mai dakin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami'ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel