A karon farko, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi magana kan haramta Twitter a Nigeria

A karon farko, Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya yi magana kan haramta Twitter a Nigeria

  • Daga karshe, Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattijai ya yi magana kan dakatar da Twitter
  • Lawan ya ce Nigeria tana bukatar Twitter kuma Twitter na bukatar Nigeria don haka yana fatar za su daidaita
  • Shugaban majalisar ya ce yana fatan gwamnati za ta yi sulhu da Twitter tunda Minista Lai Mohammed ya ce suna tattaunawa

Shugaban Majalisar Dattijan Nigeria Ahmad Lawan, a karo na farko, ya yi magana a kan dakatar da Twitter da gwamnatin tarayyar Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

A yayin da ya ke magana da manema labarai a majalisar tarayya, a ranar Juma'a, Lawan ya ce kasar na bukatar Twitter.

Shugaban Majalisar Dattijan Nigeria Ahmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria, Ahmad Lawan. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Buhari: Ainihin dalilin da yasa na naɗa Yahaya shugaban sojoji na tsallake na gaba da shi

Premium Times ta ruwaito cewa Shugaban na majalisar ya ce yana fatan gwamnatin tarayya da kamfanin Twitter za su yi sulhu.

"Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya sanar da yan Nigeria cewa suna tattaunawa da Twitter kan wannan batun. Abin da muka yi imani da shi shine Nigeria na bukatar Twitter kamar yadda Twitter ke bukatar Nigeria," in ji shi.

"Mun yi imanin cewa za a warware wannan matsalar tsakanin gwamnatin tarayyar Nigeria da Twitter.

"Ni mutum ne mai fatan ganin alheri a kowanne lokaci, na yi imanin dukkanmu mun koyi darrusan mu."

Lai Mohammed, ministan labarai da al'adu ne ya sanar da dakatar da Twitter kimanin mako guda.

Ministan ya zargi Twitter da 'barazana ga hadin kan Nigeria'.

KU KARANTA: Da Duminsa: NANS ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi ranar June 12, ta bayyana dalili

Ya dauki wannan matakin ne bayan shafin na Twitter ya goge wani sashi na rubutun Shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi wa masu tada rikici a kasar gargadi.

A yayin da majalisar ta dawo zamanta a ranar Talata, bata tattauna kan batun ba.

Amma majalisar wakilai na tarayya ta gayyaci minista Lai Mohammed kan dakatarwar amma yan majalisar ba su cimma matsaya ba kan rokon ministan a janye dakatarwar.

A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.

Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.

Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel