Dimbin ayyukan da gwamna Bala Muhammad na Bauchi yayi cikin shekaru 2 da hawa mulki

Dimbin ayyukan da gwamna Bala Muhammad na Bauchi yayi cikin shekaru 2 da hawa mulki

Shekaru biyu da suka gabata cikin watan azumi, jihar Bauchi ta yi sabon ango da ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin gwamna biyo bayan nasarar lashe zabe da gagarumar nasara.

Zaben me cike da dumbin nasarori da tarihi kasancewar sa na farko a jihar da gwamna me ci ya sha kaye yayin neman tazarce.

Yayin shan rantsuwa, sabon gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya jinjina wa daukacin al'umar jiha kan goyon baya da suka ba shi da ma jam'iyyar sa ta PDP a zaben da ya gudana kana yayi alkawarin gina sabuwar jihar Bauchi da kowa zai mora har ma jikoki da rattaba-kunne ta hanyar samar da ayyuka na Mahdi-ka-ture.

Yan magana kan ce idan Dan kaciya bai ci naman kaza ba to bai kamata yayi bara ba, abinda ya faru kenan a jihar Bauchi yar shekaru arba'in da watanni da wasu tsarorinta suka yi wa fintinkau.

Duk da cewa gwamnatin Sanata Bala Muhammad ta zo a lokacin da gwamnatin tarayya ba ta bada kudin Bail Out ko Paris Club ga kuma tarin basuka da ayyukan da suka zama alakakai daga wajen wacce ta gada, Bala Muhammad ya dukufa wajen inganta rayuwar al'umar jihar, fitattu daga cikin su kamar haka :

1. A cikin watan Yuni na shekarar 2019, mako daya bayan shan rantsuwa Gwamna Bala Muhammad ya bada kwangilar samar da wutar lantarki a Inkil da fadada lantarki a yankunan dake kewaye da Azare.

2. A cikin Juli kuwa gwamnatin ta saki Naira miliyan dari shida don sayo taki samfurin NPK ga manoma da kuma Naira miliyan ashirin da takwas da Yan kai don sayo maganin kwari.

3. An bada aikin fitacciyar hanyar Sabon Kaura zuwa Miri, Sade-Akuyam, hanyar kasuwar Muda Lawal da kuma hanyar doshe ta titin Maiduguri-Kofar Gombe cikin watan Yulin.

4. Cikin watan Agusta gwamnatin jiha ta bada aikin hanyar asibitin Azare.

5. Kwaskwarima wa hanyar Alkaleri-Gwaram-Gokaru da gina hanyoyin Yalwan Duguri-Badaran Dutse, Birim-Bajama, Kumbala-Kundak da Wurno-Burga.

6. Cikin watan Satumba gwamnatin ta gina karin wuraren zubda shara uku a fadar jiha, samar da kujerun zama a makaranti da dakunan bincike na kimiyya da kuma kwaskwarima da gina sabbin dakunan karatu a fadin jiha da kuma samar da littafan karatu da rubutu ga dalibai.

7. Watan Oktoba kuwa fannin lafiya ya samu kwayoyi da magungunan cutukan shawara da zazzabin cizon sauro, Lassa da kuma gina sabbin kananan asibotoci a wasu sassan jiha.

8. Nuwamba: gyaran makarantin kwalejin fasaha ta Gamawa da Tafawa Balewa, kayan saukaka koyo da koyarwa karkashin hukumar BESDA a kananan hukumomin Alkaleri, Gamawa, Ganjuwa da sauran su.

9. Disamba: Gyaran manyan makaranti na musamman da gina bayi, daruruwan famfunan burtsatse.

An rufe shekarar 2019 da bitar kudaden kwangilar ayyukan da tsohuwar gwamnati ta yi watsi da su inda gwamnan ya umurci dukkanin Yan kwangilar su dawo bakin aiki ko dawo da kudin gwamnati.

Duk da cewa shekarar 2020 ta zo cike da Kalubalen tattalin arziki da kuma cutar corona da ta addabi duniya, Hausawa suka ce me zuciya ake fadawa biki ba me zani ba.

Gwamna Bala Muhammad bai yi Kasa a guiwa ba wajen cigaba da samar da ayyukan cigaba da kawo sauyi ga rayuwar al'umar jihar Bauchi ba.

An ware kaso me tsoka cikin kasafin kudin shekarar 2020 kuma nan take aka fara samar da sauye sauye na musamman cikin matakan inganta tare da farfado da martabar ilimi.

Dimbin ayyukan da gwamna Bala Muhammad na Bauchi yayi cikin shekaru 2 da hawa mulki
Dimbin ayyukan da gwamna Bala Muhammad na Bauchi yayi cikin shekaru 2 da hawa mulki
Asali: Original

Fitattu cikin ayyukan Gwamna Bala cikin shekarar 2020 sun hada da:

1. Janairu: Samar da kujerun zama da kuma kayan saukaka koyo da koyarwa na daruruwan miliyoyin nairori.

2. Febrairu: Cikin wannan wata Sanata Bala Muhammad ya gina tubalin ginin da tarihi zai rubuta sunan sa da alkalamin zinare inda aka kaddamar da aikin gina gidaje dubu biyu a masarautun Bauchi, Katagum, Misau, Jamaare, Ningi da kuma Dass, ayyukan an ware biliyoyin nairori don gudanar da su da zummar samar da gidajen kananan ma'aikata akan farashi me rahusa.

3. Maris: Gwamnati ta samar da kekunan dinki da ta rabawa teloli sama da arbain baya ga biya musu kudaden haya cikin matakan horas da mata da matasa masu kananan sana'oin hannu.

An sabunta wutar tituna cikin fadar jiha da kuma gyara wadanda suka shafe shekaru ba sa aiki duk cikin wannan wata.

4. Afrilu: Gyaran wutar lantarki Makara Huta da kuma Sabon layi wadanda dukkanin su aka sanyawa sabbin injunan wuta.

Har wa yau Gwamna Bala Muhammad ya kaddamar da gina sansanin alhazan jihar a Durum, aikin wanda shine irinsa na farko a shiyyar arewa maso gabas.

5. Mayu: samar da injunan wuta a unguwar Baraya da kuma fadada lantarki a Magama-Gumau, karamar hukumar Toro.

6. Yuni: Sabunta dakin binciken/karatu na jiha zuwa na zamani.

Gyara da kwaskwarima wa wasu daga cikin manyan asibotocin jiha da kuma samar kayan yaKi da yaduwar cutar corona.

Bayar da gudummawar jari da kayan amfanin gona wa mata dari biyu da matasa dari a fadin jiha.

7. Yuli: Aikin hanyar Gwan-gwan-gwan zuwa Bakaro, Kofar Dumi -Malam Goje-Bakin kura zuwa Muda Lawal.

Gyaran gidajen malamai, dakunan karatu da wuraren kwanan dalibai a sakandiren gwamnati da ke Katagum.

Samar da lantarki a da injin wuta a Maje, karamar hukumar Ningi.

Gina bayi da daruruwan famfunan burtsatse a kananan hukumomin Alkaleri, Gamawa, Itas Gadau, Bauchi, Misau, Zaki da Jamaare.

8. Agusta: Adon tafiya dattawa suka ce waiwaye. Dalilan da suka sa Gwamna Bala Muhammad ya kafa wani kwamiti me karfi da zai sanya ido kan yadda ayyukan da gwamnatinsa suka bayar ke gudana inda kwamitin ya fara zagawa tare da sanya idanu cikin watan Agusta.

9. Satumba: cikin wannan wata a shekarar da ta gabata kungiyoyi da dama suka karrama gwamnan da lambobin yabo ciki har da fitattun jaridu da mujallu domin baya ga aikin hanyar cikin garin Bununu, gyaran hanyar Bulkachuwa, Disina da Udubo-Gamawa, Gwamna Bala Muhammad ya bada aikin kwaskwarima wa makaranti dari biyu da talatin da hudu a fadin jiha!

Kuma cikin watan ne aka gina bayi na zamani da kuma samar da kayan aiki a asibitin Bagel da gina wasu sabbi a Dass.

10. Oktoba: Cikin wannan wata aka fara tare da kammala aikin hanyar da ta tashi daga Tambari zuwa sabon titin Sabon Kaura da kuma cikin kwalejin horas da aikin jinya da ungozoma aka kuma bada aikin kwaskwarima da fadada gidan gwamnatin jiha.

Duk cikin Oktoban, an sake bada kwangilar kwaskwarima wa karin makaranti dari biyu da goma sha takwas a fadin jiha, ayyukan da yanzu sun zama kammalallu.

11. Nuwamba: An gina magudanan ruwa a Kandahar da Zango da kuma hanyoyin cikin sabon sansanin alhazan jihar Bauchi.

Daruruwan famfunan burtsatse gwamnatin ta samar cikin watan a da dama daga cikin makarantin da ta gyara da sabbin da ta gina.

Ta kuma gina salga da bayi na zamani baya ga ginin sabbin dakunan karatu.

Dimbin ayyukan da gwamna Bala Muhammad na Bauchi yayi cikin shekaru 2 da hawa mulki
Dimbin ayyukan da gwamna Bala Muhammad na Bauchi yayi cikin shekaru 2 da hawa mulki
Asali: Original

Shekarar 2021 da muke ciki :

Yanzu-yanzu sai Allah, amma inda Rabbana abin ba wahala.

1. Janairu: Gina wurin zubda shara a Ilela, kwaskwarima tare da fadada dakin taron dalibai a sakandiren gwamnati a karamar hukumar Katagum.

Aikin hanyar Karofin Madaki, Bata-Nupawa, Jaja da kuma Shagari cikin fadar jiha.

Ginin sabon asibitin Alkali Aminu, kan hanyar Gwambe.

2. Febrairu: Samar da katafariyar motar dibar shara ta zamani wa hukumar kula da tsaftar muhalli ta jiha, BASEPA.

Gina sabbin dakunan karatu a firamaren Shadawanka, barikin soji da kuma kwaskwarima wa masaukin baki dake Kaduna.

3. Maris: Watan lafiya! Gyara, kwaskwarima, da sauran ayyuka arbain gwamnati ta yi a asibitocin ta arbain a fadin jiha.

Ta kuma cigaba da gyara da samar da bayi a makaranti talatin da daya wadanda da daman su an gina musu sabbin dakunan karatu na zamani.

4. Afrilu: Gada da magunadun ruwa a Bara ba kuma samar da sabbin injunan wuta ga titunan fadar jiha.

5. Mayu: Aikin hanyar Arinja-Balma da kuma cikin garin Nasaru.

Aiki dai aiki domin tashi da wuri shi yake hana gira toho.

Lawal Muazu Bauchi

Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani

Lahadi 30 Mayu, 2021.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel