Sojojin Najeriya Sun Ragargaji Boko Haram Da Bama-Bamai a Borno

Sojojin Najeriya Sun Ragargaji Boko Haram Da Bama-Bamai a Borno

- Rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar yin kaca-kaca da maboyar 'yan Boko Haram a Borno

- Sojojin sun kashe akalla mayakan Boko Haram 40 a yayin harin da suka kai kan 'yan ta'addan

- An ruwaito cewa, an samu bayanan sirri ne da ya kai ga samun nasarar kashe tarin 'yan ta'addan

Bayan ingantattun bayanan sirri, sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun yi ruwan bama-bamai kan tarin mayakan Boko Haram a kauyen Dawuri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Jaridar PRNigeria ta tattaro cewa 'yan ta’addan suna shirin kai hare-hare ne a kewayen Maiduguri lokacin da Sojojin Najeriya suka kai hari da manyan bindigogi a sansaninsu.

Wani jami’in leken asirin soja da ke cikin aikin ya fada cewa sojojin sun fara kai hare-haren ne bayan da suka samu bayanan sirri kan motsin mayakan da kuma kutse ta hanyar sadarwar su.

KU KARANTA: Dawo-dawo: Matasan Najeriya Sun Kudiri Aniyar Tarawa Jonathan Kudin Takara a 2023

Sojojin Najeriya Sun Ragargaji Boko Haram Da Bama-Bamai a Borno
Sojojin Najeriya Sun Ragargaji Boko Haram Da Bama-Bamai a Borno Hoto: thedefensepost.com
Asali: UGC

“Baya ga sahihan bayanai daga mutane kan zirga-zirgar 'yan ta’addan, mun sami damar katse hanyar sadarwarsu da kuma mummunan shirinsu na kai hari Maiduguri da kewayen ta.

“An rusa mummunan shirin nasu lokacin da Sojojin Najeriya suka fara harba bama-bamai a cikin yankin baki daya sannan kuma suka yi sa’ar kai wa ga taron 'yan ta’addan inda suka kashe akalla 40 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da raunuka daban-daban.

"Mukaddashin Janar na runduna ta 7 na sojojin Najeriya, Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo ya yi matukar farin ciki har ya aika da kalmomin yabo da kuma karfafa gwiwa ga sojojin saboda sabon aikin."

KU KARANTA: Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani malamin addinin kirista mai suna Sydney Shirsha da wasu mutum biyu a kauyen Amudu da ke Giza a masarautar karamar Hukumar Keana ta Jihar Nasarawa.

Daily Trust a ranar Lahadi ta gano cewa ’yan bindigan da ake zargi, wadanda ke dauke da muggan makamai, sun afka wa Amudu, wani kauyen kabilar Tiv da ke yankin Giza, a tsakar daren Asabar.

Karin bayanin da aka samu ya nuna cewa harin ya bar wasu da dama da raunuka daban-daban na harbin bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel