Dawo-dawo: Matasan Najeriya Sun Kudiri Aniyar Tarawa Jonathan Kudin Takara a 2023
- Wata kungiyar matasa ta bayyana kudirinta na sayawa tsohon shugaban kasa Jonathan Fom
- Kungiyar ta bayyana kwarin gwiwar ta game da tsohon shugaban kasan da irin kokarinsa
- Ta ce shi kadai ne a yanzu zai iya magance matsalar Najeriya, don haka za su tsaya ya ci zabe
Wata kungiya karkashin inuwar kungiyar matasa mai suna 'Earnestly Demand For Goodluck E.Jonathan' (YED4GEJ 2023) ta nemi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya sake fitowa takarar shugaban kasa a 2023.
Jonathan ya rasa mulki ne a zaben shekarar 2015, wanda hakan ya kawo karshen shekaru 16 na mulkin Jam’iyyar PDP a kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar na kasa, Prince Teddy Omiloli da Daraktan Ayyuka na kasa na kungiyar, Kwamared Douye Daniel a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi sun nuna kwarin gwiwa cewa Jonathan zai magance kalubalen da ke addabar kasar idan aka ba shi dama.
KU KARANTA: Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP
Kungiyar ta bayyana cewa Jonathan ya ga bukatar sake fasalin Najeriya yayin da yake kan mulki sannan ya yi kira da a gudanar da taron tattaunawa na kasa a shekarar 2014, amma ba a ba shi damar aiwatar da shi ba, saboda faduwa da ya yi, don haka akwai bukatar sake ba shi dama.
Bayan yanke shawara tsakanin jiga-jigan kungiyar wadanda suka hada da matasa da attajirai, sun ce: “Goodluck Jonathan, dan dimokiradiyya ne na gaskiya, mai gina kasa, mai kishi da dogaro da Allah da gaskiya wanda hakan zai yi maganin matsalolin Najeriya na yanzu.
“Shi (Jonathan) ya tabbatar da cewa zai iya sadaukar da komai don tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da ci gaban babbar kasarmu Najeriya.
“Mu, a matsayinmu na matasa na wannan babbar kasa bayan gano matsalolin Najeriya muka gano mafita a cikin Goodluck Jonathan.
"Muna kira ga dukkan 'yan Najeriya ciki har da manyanmu na siyasa, masu ci a yanzu da shugabannin addinai da su shiga cikin kiran a dawo da Goodluck Ebele Jonathan kuma ku shiga tafiyarmu ta #BringbackGEJ.
"Mu matasa a shirye muke mu sayi fom din Shugaba Jonathan a kowace jam'iyya da ya zaba don tsayawa takara daga ciki kuma za mu dauki nauyin yakin neman zabensa tun daga farko har zuwa karshen lokacin da ya karbi wannan kyakkyawar kira," in ji kungiyar.
KU KARANTA: Ya Isa Haka: Saudiyya Ta Bukaci a Tuhumi Isra'ila Kan Kisan Gilla ga Falasdinawa
A wani labarin, Shugabannin darikar Tijjaniyya sun bayyana zaman tsohon Sarkin Kano, Mohammadu Sanusi II shugaban Tijjaniya alheri ga Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Malaman da suka bayyana hakan lokacin da suka kai ziyarar ban girma gidansa na Kaduna sun kuma ce duk mabiyansu a Najeriya da Afirka suna alfahari da shi.
Wakilin shugaban darikar Tijjaniyya na duniya, Sheikh Abdul-Ahad Nyass wanda ya jinjinawa tsohon sarkin ya ce shawara ce ta bai daya da kasancewar tsohon sarki sanusi a matsayin Khalifa a Najeriya.
Asali: Legit.ng