Hukunta mutane kan laifin batanci ga Annabi abin damuwa ne, Amurka

Hukunta mutane kan laifin batanci ga Annabi abin damuwa ne, Amurka

- Sakataren wajen Amurka ta soki gwamnatin Buhari kan kisan yan Shi'a a Zariya

- Zaku tuna cewa a Disamban 2015, an hallaka mabiya akidar Shi'a da dama a garin Zazzau

- Har yanz babu wanda aka kama da laifi illa shugaban 'yan Shi'an Zakzaky

Kasar Amurka ta bayyana damuwarta kan yadda kotuna a Najeriya ke cigaba da hukunta masu laifin batanci ga Annabi, ta hanyar jefasu kurkuku da yanke musu hukuncin kisa.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rahoton yancin addini na 2020, rahoton Punch.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya har yanzu bata hukunta wadanda suka hallaka mambobin kungiyar Shi'a da aka yiwa kisan gilla a shekarar 2015 ba amma tana hukunci masu laifin batanci.

"A Najeriya, kotuna na cigaba da hukunta masu batanci ga addini, ana jefasu gidan yari na wa'adi mai tsawo kuma ana yanke musu hukuncin kisa. Duk da haka gwamnati bata hukunta Sojojin da suka kashe daruruwan yan Shi'a a 2015 ba," Blinken ya karanto cikin rahoton.

DUBA NAN: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Hukunta mutane kan laifin batanci ga Annabi abin damuwa ne, Amurka
Hukunta mutane kan laifin batanci ga Annabi abin damuwa ne, Amurka
Asali: UGC

DUBA NAN: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Chadi, Mahamat Deby

Ya kara da cewa yancin addini hakki ne na bil adama kuma yace Amurka za ta cigaba da kare hakkin addini a fadin duniya.

"Yancin addini, kamar kowani hakkin bil adama, abune da ya game duniya. Kowa a ko ina na da hakkin imani da abu da kuma kafirce masa," Blinken ya kara.

A bangare guda, Ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Afrika ta kudu ta sanar da cewa tana shirin kafa sabuwar dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya kamar yadda maza ke auren mace fiye da daya.

A cewar rahoton iharare, sabuwar dokar za tayi bayani game salon auratayyan da basu hallata ba.

Rahoton yace takardar da ma'aikatar ta fitar wannan makon ya nuna cewa babu adalci da daidaito kan dokar auren da ake amfani da shi yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng