Allah mai iko akuya ta haifi dodo bayan an yi mata tiyata

Allah mai iko akuya ta haifi dodo bayan an yi mata tiyata

- A ranar Litinin da ta gabata ne wani abun mamaki ya faru a garin Ilesha na jihar Osun

- Wata akuya aka yi wa aiki don tseratar da ranta daga halaka amma sai aka ciro wata halitta mai kama da dodo

- Halittar na da kafafu takwas amma jim kadan bayan an fito da ita sai ta ce ga garinku

A ranar Litinin da ta gabata ne wani abin al'ajabi da mamaki suka faru a garin Ilesha na jihar Osun. Wata akuya ce ta haifi wata irin halitta mai kama da dodo bayan an yi mata tiyata.

Kamar yadda jaridar aminya Daily Trust ta ruwaito, likitan da yayi wa akuyar tiyata mai suna Dakta Afolabi Joseph ya shaida cewa anyi aikin ne don ceto ran akuyar. Ya tabbatar da cewa an yi aikin tiyatar ne cikin nasara.

Hakazalika, sakatariyar hulda da manema labarai ta ma'aikatar noma a jihar Osun, Segilola Babalola ta shaidawa Aminiya cewa halittar da akuyar ta haifa na da kafafu takwas. A cewarta, halittar na kama da dodo kuma ta mutu ne jim kadan bayan an haifeta amma uwar na nan da ranta.

KU KARANTA: Tashin hankali: An tsinci gawar mutumin da yayi kokarin kashe shugaban kasa

A daya bangaren kuma mun kawo muku labarin wata Bahaushiyar budurwa da ta ce ta shafe tsawon watanni shida tana nazari akan addinin kiristanci.

Budurwar mai suna Fatima Yusuf, ta ce tana boyewa ne ta karanta littafin, yayin da kuma a duk lokacin da ta karanta shi take samun nutsuwa sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel