Shugaba Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Chadi, Mahamat Deby
- Bayan kisan mahaifinsa, Mahamat Debu ya dane kujerar mulkin kasar Chadi
- Hawarsa mulki ke da wuya, ya fara kai ziyara wajen shugabannin kasashen da ke mawabtaka da Chadi
- Wannan karon ya kawo ziyararsa ta farko Najeriya a ranar Juma'a
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, ya karbi bakuncin dan marigayi Idris Deby, Mahamat Kaka Deby, wanda shine mukaddashin shugaban kasar Tchad.
Janar Mahamat ya dira fadar Aso Villa ne misalin karfe 11:11 na safe, rahoton TheNation.
Duk da cewa ba'a san abinda suke tattaunawa ba a yanzu, ana kyautata zaton yana da alaka da matsalar tsaro na yan ta'addan Boko Haram a yankin Sahel.
Mahamat Deby ya gaji mahaifinsa ne wanda yan tawaye kasar Chadi suka hallaka a filin daga.
Kalli hotunan:
KU KARANTA: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari
KU DUBA: Wajibi ne Buhari ya saurari abinda muke fada masa, Gwamnonin Kudu 17
A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya bayyana cewa gwamnatinsa na namijin kokarin wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.
A bayaninsa, Buhari yace yana fatan yan Najeriya zasu gane irin kokarin da sukeyi.
Buhari ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai bayan halartan Sallar Idi a fadar shugaban kasa, Aso Villa, Abuja.
Asali: Legit.ng