Kasar Afrika ta kudu na shirin kafa dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya

Kasar Afrika ta kudu na shirin kafa dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya

- Duniya juyi-juyi, ga wata sabuwa da kasar Afrika ta kudu

- Gwamnatin kasar na shirin kafa sabuwar doka domin daidaito tsakanin maza da mata

- Abinda aka sani shine namiji ya auri mata har hudu, amma yanzu ana son halastawa mata aure maza barkatai

Ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Afrika ta kudu ta sanar da cewa tana shirin kafa sabuwar dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya kamar yadda maza ke auren mace fiye da daya.

A cewar rahoton iharare, sabuwar dokar za tayi bayani game salon auratayyan da basu hallata ba.

Rahoton yace takardar da ma'aikatar ta fitar wannan makon ya nuna cewa babu adalci da daidaito kan dokar auren da ake amfani da shi yanzu.

Daga cikin rashin adalcin shine dokar bata hararo salon auren mabiya addinin Hindie, Yahudu, Musulmi da Rastafarian ba.

Takardar ta bukaci a sanya sabon slon aure inda mace za ta samu yancin auren namiji fiye da daya.

DUBA NAN: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Kasar Afrika ta kudu na shirin kafa dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya
Kasar Afrika ta kudu na shirin kafa dokar halastawa mata auren namiji fiye da daya
Asali: Facebook

DUBA NAN: An damke tsagerun yan bindiga 5 a Zamfara da muggan makamai

Sarakunan gargajiya a kasar Afrika ta kudu sun nuna rashin amincewarsu da wannan shiri da akeyi inda suka bayyana cewa "wannan abu ya sabawa al'adar al'ummar Afrika."

Amma ma'aikatar ta mayar da martanin cewa: "Abin takaici shine wadanda suka yarda namiji ya auri mace fiye da daya ne suke adawa da mace ta auri namiji fiye da daya."

Rahotanni sun cewa an baiwa yan kasar zuwa karshen watan Yuni su tofa albarkatun bakinsu kafin a yanke shawara kan lamarin.

A bangare guda, an amince a sha shisha a wuraren shan gahawa a Saudiyya daga ranar Litinin yayin da ake sassauta dokar kullen korona a ƙasar, rahoton Saudi Gazzete.

Bayan shekara guda, Saudiyya ta fara sassauta dokokin kulle sakamakon annobar cutar Korona.

Cikin sharrudan da ma’aikatar kula da birane da karkara ta gindaya domin amincewa mutum ya shiga shagon Shisha shine ya kasance ya yi rigakafin Korona. Read more:

Asali: Legit.ng

Online view pixel