TUC Ta Nemi Gwamnatin Kaduna Ta Biya Ma’aikatan da Ta Kora Hakkokinsu
- Kungiyar kwadago a jihar Kaduna ta nemi gwamnati ta biya wadanda ta kora daga aiki hakkokinsu
- Ta kuma bukaci wadanda suka yi ritaya ma a basu masu don rage radadin talauci da rashin ayyukan yi
- Hakazalika kungiyar ta karyata jita-jita da ke yawo cewa za a sallami ma'aikatan gwamnati da suka haura shekaru 50
Kungiyar kwadago reshen jihar Kaduna (TUC) ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta biya hakkokin dukkan wadanda suka yi ritaya da kuma ma’aikatan da lamarin kora ya shafa kwanan nan.
Kungiyar kwadagon ta ce biyan zai magance matsin tattalin arzikin da suke fama dashi da kuma rage radadin rashin ayyukan yi, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: An Kama Wasu Ma’aikatan Gwamnati Daga Cikin ’Yan Bindiga a Jihar Zamfara
Shugaban kungiyar na jihar, Kwamared Abdullahi Danfulani da ya bayyana hakan a wani taron manema labarai don bikin ranar ma’aikata, ya ce yana da matukar ciwo a sallami mutum daga aiki ko kuma ya yi ritaya daga aiki ba tare da an biya shi hakkokinsa ba.
Danfulani, ya karyata jita-jitar da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta na cewa gwamnatin jihar na shirin rage ma'aikata masu shekaru 50 zuwa sama daga Ma’aikatan Gwamnati.
KU KARANTA: An Tsinci Gawar Wani Yaron da Aka Sace a Magudanar Ruwa Bayan Biyan Fansa
Kungiyar ta ce gwamnatin Nasiru El-Rufai ta kori ma'aikata 30,000 tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2015.
Babban sakataren kungiyar hadaka ta AUPCTRE, Comrade Sikiru Waheed, shi ne ya bayyana haka yayin bikin ranar ma'aikata a Abuja.
Asali: Legit.ng