Buhari Bai Damu da Halin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki Ba, PDP Ta Caccaki Buhari

Buhari Bai Damu da Halin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki Ba, PDP Ta Caccaki Buhari

- Jam'iyyar PDP ta koka kan yadda gwamnatin Buhari ke nuna halin ko in kula game da matsalar 'yan Najeriya

- A cewar PDP, gwamnatin Buhari ba ta damu da matsalar da Najeriya ke fuskanta ba a cikin kwanakin nan

- PDP ta ce jam'iyyar APC da gwamnatin Buhari sun fi mayar da hankali kan cin zaben shugaban kasa na 2023

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta damu da 'yan Najeriya ba shi yasa ake samun karuwar masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga da ke cin karensu babu babbaka a sassan kasar.

PDP da take mayar da martani kan halin da Najeriya ke ciki ta matsalar tsaro, ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kakakinta Kola Ologbondiyan ya fitar.

Kakakin ya koka kan yadda Shugaba Buhari yaki fitowa ya ce komai a lokacin da kasar ke cikin wani yanayi na matsi tare da zargin shugaban na ba da gudummawa a kara tabarbarewar tsaro a kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana

Ba ruwan gwamnatin Buhari da talakawan Najeriya, PDP ta caccaki Buhari
Ba ruwan gwamnatin Buhari da talakawan Najeriya, PDP ta caccaki Buhari Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

A cewar PDP, babban abin da APC da gwamnatin Buhari suka mayar da hankali a kai shi ne yadda za su lashe zaben 2023 -ba sa duba yadda 'yan bindiga suke abin da suka ga dama da kisan al'umma kusan kullum.

"Saboda rashin jagoranci da rashin imani da rarrabuwar kan gwamnatin Buhari, rikici, kashe-kashe da tashin hankali suna ta karuwa a kasar.

"Alamun gazawa ne yadda gwamnatin Buhari da APC ke nuna rashin damuwa yayin da 'yan bindiga da 'yan fashin daji ke cin kasuwa a wasu yankunan kasar har ma ta kai sun kafa tuta a Shiroro da ke jihar Neja, wanda yake nisan wajen Abuja, babban birnin Najeriya taku 200 ne.."

A cewar PDP, ya kamata 'yan Najeriya su yi duba ga irin zafafan kalaman da aka yi musayarsu tsakanin Sanata Remi Tinubu da Sanata Smart Adeyemi na APC wanda ya fito karara ya nuna yadda gwamnatin Buhari ta gaza a harabar majalisar dattawa.

Sai dai, sanata Tinubu ta gargadeshi yadda shi ba dan PDP ba amma yake fitowa yana fadin irin wadannan kalaman a matsayinsa na wanda ya fito daga jam'iyya mai mulki, kamar yadda sanarwar ta sanar.

KU KARANTA: Babu Shugaban da Zai So Kasarsa Ta Lalace, Ku Dai Ku Hada Kai, Tinubu Ga ’Yan Najeriya

A bangare guda, Shugabannin Evangelical Church Winning All (ECWA) sun nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus daga kujerarsa idan ba zai iya kawo karshen satar mutane ba, yayin da suka binne dalibin Jami’ar Greenfield da masu satar mutane suka kashe a jiya.

Duruwan mutane sun koka cikin masu makoki da suka halarci jana’izar wata daliba jami’a, Dorathy Yohanna, a cocin ECWA Goodness, da ke Jihar Kaduna, inda malamai da dangin marigayiyar suka bukaci gwamnati da ta ceci Najeriya daga hannun 'yan ta'adda.

Mataimakin Sakatare Janar na ECWA, Rev. Samuel Atu, ya koka kan yadda gwamnatin tarayya da ta jihohi ke nade hannu yayin da kasar ke cikin tashin hankali, The Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel