Za Mu Yi Kira Ga Tsige Buhari Idan Aka Gagara Samun Mafita, Majalisar Tarayya

Za Mu Yi Kira Ga Tsige Buhari Idan Aka Gagara Samun Mafita, Majalisar Tarayya

- Wani dan majalisar tarayya ya bayyana ikon majalisar kan batun tsige shugaba Muhammadu Buhari

- Ya bayyana cewa, idan bangaren zartarwa ta gagara aiki da kudurin tsaro, to za ta bijiro da batun tsige shugaban

- Sai dai, alamu na nuna tsige shugaban abu ne mai wahala kasancewar jam'iyyarsa ke jagorantar majalisun

Wani dan majalisar tarayya a ranar Alhamis ya ce Majalisar Dokoki ta kasa za ta bijiro da batun tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan bangaren zartarwa ba ta yi aiki da kudurin ta na tsaro ba.

Majalisar wakilai a ranar Laraba ta kaddamar da wani kwamiti na mutune 40 don samar da mafita ga kalubalen tsaron kasar.

Kwamitin zai shirya taron kwanaki hudu na tsaro a watan Mayu.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily, dan majalisar mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a majalisar Tarayya, Dachung Bagos ya ce za a bijiro da batun tsigewar ne idan ba a zartar da kudurorin taron koli ta bangaren zartarwa ba.

KU KARANTA: Buhari Bai da Damu da Halin Da ’Yan Najeriya Ke Ciki Ba, PDP Ta Caccaki Buhari

Za mu yi kira ga tsige Buhari idan lamauran tsaro suka ta'azzara, Majalisar tarayya
Za mu yi kira ga tsige Buhari idan lamauran tsaro suka ta'azzara, Majalisar tarayya Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

"Idan bangaren zartarwa ta aiwatar da kashi 30 cikin dari na mafita da shawarwari da Majalisar Kasa ke bayarwa, zan iya tabbatar muku da ba za mu iya kaiwa ga wannan matakin ba," in ji shi.

Maimakon haka, ya kara da cewa, bangaren zartarwa ta siyasantar da batun rashin tsaron kasar.

Ya kuma bayyana taron da za a gudanar a matsayin "makoma ta karshe."

"Bayan wannan taron, idan ba a yi komai ba - tattaunawa mai zurfi, kashe kudade don samar da mafita - idan bangaren zartarwa ba ta yi komai ba bayan wasu watanni, to tabbas za mu yi kira ga Shugaban ya yi murabus," in ji shi.

"Muna da ikon tsige shugaban kasa idan har ba zai iya tsare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya ba."

Sai dai a bangare guda, tsige shugaban kasa abu ne mai matukar wuya saboda dukkannin majalisun wakilai da na dattijai suna karkashin jam'iyyar APC ne.

KU KARANTA: Gwamnatin Katsina ta Gaggauta Haramta Wasannin 'Tashe' da Ake a Ramadana

A wani labarin daban, Shugabannin Evangelical Church Winning All (ECWA) sun nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus daga kujerarsa idan ba zai iya kawo karshen satar mutane ba, yayin da suka binne dalibar Jami’ar Greenfield da masu satar mutane suka kashe a jiya.

Duruwan mutane sun koka cikin masu makoki da suka halarci jana’izar wata dalibar jami’a, Dorathy Yohanna, a cocin ECWA Goodness, da ke Jihar Kaduna, inda malamai da dangin marigayiyar suka bukaci gwamnati da ta ceci Najeriya daga hannun 'yan ta'adda.

Mataimakin Sakatare Janar na ECWA, Rev. Samuel Atu, ya koka kan yadda gwamnatin tarayya da ta jihohi ke nade hannu yayin da kasar ke cikin tashin hankali, The Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel