Sheikh Gumi Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Sakamakon Tattaunawar da Ya Yi Da ’Yan Fashi

Sheikh Gumi Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Sakamakon Tattaunawar da Ya Yi Da ’Yan Fashi

- Sheikh Gumi ya yi magana game da sakamakon tattaunawar da ya yi da 'yan fashi da ke addabar yankin arewacin kasar

- Malamin addinin musuluncin ya ce 'yan bindigar da ya hadu dasu sun daina garkuwa da mutane

- Sai dai, Gumi, ya koka kan yadda hukumomi suka dakatar da tattaunawar sulhu da ya keyi da 'yan ta'addan

Sheikh Ahmed Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya sake kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi afuwa ga ‘yan bindigar da ke yin barna a fadin arewacin Najeriya.

Sheikh Gumi wanda a kwanaki ya kasance kan gaba a tattaunawa da 'yan fashi ya ce wadanda ya hadu da su a baya sun tuba.

Malamin addinin musuluncin ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Roots wanda aka wallafa a shafin Youtube.

Sheikh Gumi Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Sakamakon Tattaunawar da Ya Yi Da ’Yan Fashi
Sheikh Gumi Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Sakamakon Tattaunawar da Ya Yi Da ’Yan Fashi Hoto: @engr_zHaruna
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gbajabiamila Yayi Magana Game da Matsalar Tsaron Najeriya, Ya Bayyana Abin da Buhari Ke Fama da Shi

Kalaman nasa: “Duk wadanda muka hadu da su, dukkansu sun daina harkar garkuwa da mutane. Wadanda suke yi a yanzu wasu 'yan damfara ne wadanda ba mu zauna da su ba."

Sheikh Gumi ya kara da cewa tsarin “zama tare” da sauran ‘yan fashi ya samu cikas daga hukumomin da ba sa so.

Lokacin da aka tambaye shi game da rashin adalcin da ake gani a kan wadanda 'yan ta'addan suka cuta tare da neman afuwa, malamin na Islama ya ce shi ma aikin yan ta'adda ya taba shafarsa.

Ya ce an sace dan uwansa kuma an biya kusan naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa don ceto shi.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-duminsa: Buhari ya gana da Zulum kan rashin tsaro

A gefe guda, Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ce al’ummar kasar za su yi nadama idan aka tsige Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani daga mukaminsa, TheCable ta ruwaito.

Yawancin 'yan Najeriya da kungiyoyi suna ta rokon Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Pantami bayan bidiyo da aka nuna a shekarun 2000 sun sake bayyana inda aka ga ministan yana goyon bayan Al-Qaeda da Taliban.

Pantami, duk da haka, ya sake tunani game da tunaninsa na baya-bayan nan game da kungiyoyin ta'addancin, yana mai cewa matsayinsa a lokacin ya dogara ne da fahimtarsa lokacin da yake saurayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel