Gbajabiamila Yayi Magana Game da Matsalar Tsaron Najeriya, Ya Bayyana Abin da Buhari Ke Fama da Shi

Gbajabiamila Yayi Magana Game da Matsalar Tsaron Najeriya, Ya Bayyana Abin da Buhari Ke Fama da Shi

- Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a ranar Litinin, 26 ga watan Afrilu, ya gana da Shugaba Buhari a fadar shugaban kasa

- Gbajabiamila ya bayyana cewa tattaunawarsa da shugaban na Najeriya ya ta'allaka ne kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar

- A cewar kakakin, duba ga yanayin tsaro a Najeriya, shugaban kasa na fama da mawuyacin hali

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari na fuskantar wani mawuyacin hali domin ya shafi matsalolin tsaro a kasar.

Channels TV ta ruwaito cewa ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin bayan wata ganawar sirri da shugaban kasar a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin tarayya (FCT).

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Yadda El-Rufai Ya Nemi Jonathan Ya Tattauna Kan Sakin 'Yan Matan Chibok

Gbajabiamila Yayi Magana Game da Matsalar Tsaron Najeriya, Ya Bayyana Abin da Buhari Ke Fama da Shi
Gbajabiamila Yayi Magana Game da Matsalar Tsaron Najeriya, Ya Bayyana Abin da Buhari Ke Fama da Shi Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Twitter

Da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa, kakakin maalisar ya bayyana cewa ya je fadar Villa ne domin tattaunawa tare da Shugaba Buhari kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar.

“Mun yi magana kan tsaro, mun yi magana kan tattalin arziki, mun yi magana game da siyasa, kuma yana sauraronmu idan muka gabatar da dabaru; ya fada mana nasa ra'ayin kuma mun cimma matsaya daya a cikin haka,” in ji shi.

A halin da ake ciki, a ranar Litinin, Jam'iyyar APC tace bada jimawa ba shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa zasu yi maganin duk wani dake da hannu a ƙaruwar matsalar tsaron ƙasar nan.

Ta ce wannan yanayin na rashin tsaro abun damuwa ne matuƙa, saboda haka jam'iyyar ba zata saka siyasa a lamarin da ya shafi rayuwar yan Najeriya ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Pantami: NSCIA Ta Caccaki CAN, Tace Tsohon Ministan Kirista Ya Bayar da Belin Wanda Ya Kafa Boko Haram Sau 3

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da APC ta fitar, wadda aka yiwa take da "Ya zama wajibi mu haɗa kai domin magance rashin tsaro-APC" ɗauke da sa hannun sakataren jam'iyyar, John Akpanudoedehe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel