Tashe-tashen Hankula Sun Karade Ko'ina a Najeriya Yayin Da Wasu 'Yan Bindiga Suka Kashe 'Yan Sanda 9 a Kebbi
- Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an‘ yan sanda tara a jihar Kebbi
- Yan ta’addan sun kuma kashe mambobin kungiyar yan banga guda biyu a garin da suka kai mamaya
- Ba a nan aka tsaya ba, miyagun sun kwashe dabbobi da kayan abinci mallakar mutanen karkaran bayan harin
Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kebbi ta tabbatar da kisan wasu jami'anta tara ciki har da wani babban jami’in dan sanda (DPO) da wasu 'yan bindiga suka yi a karamar hukumar Sakaba ta jihar.
Nafi’u Abubakar, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ya ce an kashe jami’an ne a yayin artabu da ‘yan ta’addan a ranar Lahadi, 25 ga Afrilu.
'Yan banga biyu na yankin da kuma wasu da ba a san adadin su ba sun rasa rayukansu yayin harin.
KU KARANTA KUMA: Jami'ar Greenfield: Daga karshe sunaye da hotunan ɗaliban da aka kashe sun bayyana
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rahoto cewa yan fashin sun kai hari kauyuka biyar wadanda suka hada da Dankolo, Sakaba, Makuku, Dokar Kambari, da Kurmin Hodo.
Wani mazaunin kauyen, Salisu Adamu, ya ce:
“‘Yan bindiga sun far wa kauyukan mu tun da misalin karfe 8:00 na safe suka kwashe dubban shanu daga kauyukan Dankolo, Sakaba, Makuku, Dokar Kambari, da kauyukan Kurmin Hodo da kayan abinci da yawa yayinda suka zo da babura sama da 100, dauke da makamai.
"Sun fara harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya sa mutanen kauyen suka tsere don neman tsira ta fuskoki daban-daban."
KU KARANTA KUMA: Da Dumi-Dumi: Boko Haram Ta Kafa Tuta a Ƙauyen Jihar Niger
A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa wasu ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai 60 a safiyar ranar Laraba sun mamaye wani sansanin sojoji da ke garin Zazzaga, Munya, Jihar Neja.
A yayin harin, mayakan sun yi artabu da sojoji, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dama.
Harin na baya-bayan nan da aka kai kan wani sansanin sojoji a jihar ya zo ne kusan makonni uku bayan da wasu gungun ‘yan fashi suka kai hari kan rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da ke Allawa da Basa a Shiroro, inda suka kashe sojoji biyar da wani dan sanda.
Asali: Legit.ng