Yan bindiga sun sake kai hari wani sansanin sojoji a jihar Neja
- Wasu mahara da yawansu ya kai 60 sun kai farmaki wani sansanin sojoji da ke garin Zazzaga, Munya, Jihar Neja
- Sai dai kuma sun kwashi kashinsu a hannu bayan artabu da suka yi da sojojin wadanda suka yi musu laga-laga
- Ba a rasa ran ko soja guda ba amma an kaddamar da batan wani jami'in soja a sansanin
Wasu ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai 60 a safiyar ranar Laraba sun mamaye wani sansanin sojoji da ke garin Zazzaga, Munya, Jihar Neja.
A yayin harin, mayakan sun yi artabu da sojoji, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dama.
Harin na baya-bayan nan da aka kai kan wani sansanin sojoji a jihar ya zo ne kusan makonni uku bayan da wasu gungun ‘yan fashi suka kai hari kan rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da ke Allawa da Basa a Shiroro, inda suka kashe sojoji biyar da wani dan sanda.
KU KAARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sandan Enugu, an kashe jami’ai uku
Ba kamar mamayewar Allawa da Basa ba, babu wani soja da aka kashe a wannan sabon harin; sai dai, an tabbatar da batan wani soja a daidai lokacin kawo wannan rahoton, jaridar Sun ta ruwaito.
A cewar wata majiya mai tushe kusa da garin Zagzaga, ‘yan fashin sun afka wa yankin da misalin karfe 4:00 na asuba inda suka raba kansu gida uku.
Yayin da kungiya daya ta kama hanya kai tsaye zuwa sansanin sojoji da ke karamar makarantar sakandare kimanin mita 500 daga garin inda suka yi artabu da sojoji, rukuni na biyu sun yi kwanton bauna a kan babbar hanyar da zai sada mutum da garin.
An tattaro cewa rukuni na uku sun yi hanyar zuwa cikin garin don hana duk wani mataki daga 'yan banga da matasa masu aikin sa kai.
Majiyarmu ta ce bayan kimanin sa’o’i biyu na musayar wuta daga karfe 4:00 na safe zuwa 6:00 na safe, alburusai sun kare ma sojoji kuma hakan ya sa suka ja da baya amma har sai da suka yi wa ‘yan fashin mummunan rauni.
Bayan sojoji sun ja da baya, rahotanni sun ce 'yan fashin sun kutsa kai sansanin, sun cinna wa daya daga cikin motocin sojojin wuta sannan suka tafi da wani. 'Yan fashin sun kuma kona gidan abincin da ke sansanin.
KU KARANTA KUMA: Mata ta haifi yan uku bayan shekaru 11 da aure da yin bari sau 6
“Ina ganin‘ yan fashin na iya amfani da motar soji wajen kwashe wadanda suka jikkata da kuma watakila wasu da suka mutu a cikinsu saboda sojojin sun basu kashi sosai har zuwa lokacin da harsasansu suka kare,” in ji majiyar.
‘Yan fashin sun zo da misalin karfe 4:00 na safe kuma tun daga wannan lokacin muna ta jin karar harbe-harbe har zuwa misalin karfe 6:00 na safiyar yau,’ in ji shi.
A gefe guda, ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi, ya umarci rundunar 'yan sanda da ta kawar da masu tayar da hankali a yankin kudu maso gabas da sauran wurare a Najeriya.
Dingyadi a ranar Litinin, 19 ga Afrilu, ya bayyana cewa ya ba da umarnin gudanar da binciken kwakwaf a kan masu laifin da ke kai hare-hare kan 'yan sanda.
Ya yaba wa shiyya ta 13, hedkwatar ta rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambara kan dakile wani hari a daren Litinin wanda ya kai ga gano bindigar GPMG da ‘yan bangan suka yi amfani da ita.
Asali: Legit.ng