Da Dumi-Dumi: Boko Haram Ta Kafa Tuta a Ƙauyen Jihar Niger

Da Dumi-Dumi: Boko Haram Ta Kafa Tuta a Ƙauyen Jihar Niger

- 'Yan kungiyar Boko Haram sun kafa tuta a kauyen Kaure da ke karamar hukumar Shiroro na jihar Niger

- Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar ne ya sanar da hakan a jawabin da ya yi yayin da ya ziyarci sasanin yan gudun hijira a Minna

- Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dade tana neman taimakon gwamnatin tarayya kan batun tsaro amma har yanzu hakarsu bata cimma ruwa ba

'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram ta kafa tuta a kauyen Kaure da ke Shiroro a karamar hukumar jihar Niger, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci sansanin yan gudun hijira da ke makarantar frimare na IBB da ke kusa da fadar sarki a Minna.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Ƴan bindiga sun afka jami'a sun sace ɗalibai a Makurɗi

Da dumi-dumi: Boko Haram ta kafa tuta a kauyen jihar Niger
Da dumi-dumi: Boko Haram ta kafa tuta a kauyen jihar Niger
Asali: Original

An sauya makarantar frimarin zuwa sansanin yan gudun hijira cikin gaggawa bayan kimanin mutane 5000 sun baro kauyukansu a kananan hukumomin Shiroro da Munya saboda harin yan ta'adda.

Bello ya ce, "Ina tabbatar da cewa akwai yan Boko Haram a kusa da kananan hukumomin Shiroro da Kaure a jihar Niger. Sun kwace garin, sun kafa tutarsu."

Ya yi gargadin cewa yan Boko Haram din na son mayar da Kaure ya zama gidansu da kuma hedkwatarsu kamar yadda suka yi wa dajin Sambisa, inda ya kara da cewa Sambisa na da nisa sosai daga Abuja amma Kaure awa biyu ne kawai tsakaninsa da Abuja a mota.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta dade tana neman taimakon gwamnatin tarayya domin taya ta magance kallubalen tsaro inda ya kara da cewa hakar nasu bai cimma ruwa ba.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: