Muna son ganin Buhari: Mata 'yan kasuwa sun koka kan tsadar abinci
- Matan 'yan kasuwa a Najeriya basu dauki karin farashin kayan abinci abin dariya ko murna ba
- ‘Yan kasuwa mata sun koka kan hauhawar farashin kayan abinci dake shafar kasuwancinsu
- Dangane da wannan ne 'yan kasuwa ke neman ganawa da shugaba Buhari dan tattauna mafita
Karin farashin abinci a Najeriya na zama abinda ba za a iya jurewa ba, ba iya ga masu saye ba har ma ga masu sayar da kayayyakin abinci.
Wata mata ‘yar kasuwa da ta zanta da Legit.ng kwanan nan ta bayyana cewa yawan mutanen da ke rokon abinci a wannan zamanin sun fi wadanda suke da halin da za su ci da kansu.
Matar 'yar kasuwa da ba ta bayyana sunan ta ba ta bayyana cewa yana da matukar wahala da tsada a yanzu a ciyar da karamin iyalin da kudin shigansu na wata-wata bai wuce mafi karancin albashin N30,000.
KU KARANTA: Akume ya bayyana dalilan da suka sa aka gagara dakile matsalar 'yan bindiga
A cewar ta, iyalai na iya kashe kusan N5,000 a kowace rana kan abinci duba da yadda kasuwanni suke a yanzu.
'Yar kasuwar ta ce duk da cewa tana da kudin da za ta iya sayen kayan abinci, amma tana jin tausayin wadanda ba su kai matakin kudi irin nata ba.
Ta ba da misali da wata karamar leda ta Semovita wacce ta kara farashi daga N350 zuwa N450, tana mai cewa hakan na faruwa ne saboda kwadayi da son kai daga wasu mutane.
A matsayin hanyar ci gaba, ta ce idan haduwa da Shugaba Muhammadu Buhari zai iya magance matsalar, ya kamata mata 'yan kasuwa su yarda su yi hakan.
Da take mayar da martani ga shawarar kididdigar farashi da sake duba farashin a kasuwanni, ta ce hakan zai zama tunani mai kyau tunda zai amfani kowa.
Wata 'yar kasuwar ta koka cewa wani lokaci ita da abokan kasuwancinta sai sun ranta kudi domin su sayi abin da suke sayarwa saboda karin farashin ya shafi uwar kudinsu.
Ta bayyana cewa sabanin abin da ake iya samu ada, buhun yalo yanzu N12,000 ne yayin da dan kadan da ake bayarwa a da a N50 yanzu N100 ne.
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan gini guda uku a jihar Ondo
A wani labarin, Jam’iyya mai mulki ta APC ta yi ikirarin cewa babu wata gwamnati da ta taba yiwa Najeriya da 'ya'yanta aiki fiye da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yanzu.
Wannan ya fito ne daga mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Mai Mala Buni a ranar Talata, 20 ga Afrilu a Abuja.
Buni, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Yobe, ya yi wannan bayanin ne a wajen taron tattaunawa da manema labarai na kungiyar kwararrun jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng