‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan gini guda uku a jihar Ondo

‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan gini guda uku a jihar Ondo

- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aikatan aikin gini a wani yankin jihar Ondo

- Rahotanni daga rundunar 'yan sanda sun bayyana cewa, an sace mutanen ne ranar Talata

- Tuni hukumar 'yan sandan ta bada umarnin nemo wadanda aka sacen tare da kame barayin

'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma'aikatan gini a wani yankin jihar Ondo a ranar Talata da ta gabata.

Wadanda lamarin ya rutsa da su na daga cikin wadanda ke aikin gyara yankin Ikaram/kunnu -Akoko na kananan hukumomin Akoko ta Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ondo, DSP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Laraba, sannan ya kara da cewa an sace ma’aikatan ne a ranar Talata.

KU KARANTA: Najeriya na tarwatsewa farfesoshi na iya komawa aiki a gidan Burodi, Lai Mohammed

‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan gini guda uku a jihar Ondo
‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan gini guda uku a jihar Ondo Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Ya lura cewa biyu daga cikin ma’aikatan da aka sace sun fito ne daga yankin kudu maso yammacin kasar, yayin da na ukun ya fito daga jihar Filato.

A cewarsa, Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Salami ya ba da umarnin tura 'yan sanda zuwa yankin don nemowa da kuma kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su tare da cafke wadanda suke 'yan bindiga.

Kakakin 'yan sandan ya yi bayanin cewa sauran jami'an tsaro, 'yan uwa kamar Sojojin Najeriya, da na Hukumar tsaro ta NSCDC da mafarautan cikin gida suma suna cikin aikin.

Ya yi kira ga mazauna yankin da ma jihar baki daya, da su kasance a ko da yaushe tare da kai rahoton duk wani wanda ba su yarda da shi ba da suka lura da shi ga ‘yan sanda a kan lokaci.

KU KARANTA: Najeriya na tarwatsewa farfesoshi na iya komawa aiki a gidan Burodi, Lai Mohammed

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga sun sace daliban da ba a san adadin su ba daga Jami’ar Green Field da ke jihar Kaduna.

Jaridar TheCable ta fahimci cewa 'yan bindigan sun farma makarantar ne da tsakar daren Talata. An ce sun bude wuta ne don tsoratar da mazauna yankin kafin su sace wasu daliban.

Jami’ar mai zaman kanta tana kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuka a karamar hukumar Chikun, daya daga cikin wuraren da ‘yan bindiga suke a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel